Matsalar shaye-shayen mata ta fara sauki a Kano, sai dai, Katsina ta dauka

Matsalar shaye-shayen mata ta fara sauki a Kano, sai dai, Katsina ta dauka

- Adadin masu shaye shaye a jihar Katsina ya kara bunkasa musamman a bangaren matan aure

- Wasu daga cikin matan sunce suna shan wadannan abubuwa ne dan su gamsar da mazajen su

- A shekarar data gabata an kama mutane 186 masu wannan sana'ar da kuma babbar mota mai dauke da kwalabe 24,000

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Source: Facebook

Jihar Katsina ta shiga wani hali a sanadiyyar hauhawar masu shaye shaye a jihar.

A halin yanzu lamarin yafi ta'azzara ne a bangaren matan aure,dalibai da kuma yan mata.

Jaridar Legit ta rawaito mana cewa matan aure da yan mata a jihar Katsina suna shan maganin tari,wiwi da kuma sauran magunguna kamar Rophynol, tramadol, diazepan da kuma lexotan wadanda magunguna ne da suke da ka'ida ba'a siyar dasu idan ba likita ne ya rubuta ba.

Wadannan magunguna an samar dasu ne saboda masu ciwon sikila amma sai mutane suke amfani dasu wajen gusar da hankulan su.

Masu sana'ar saida magani a kasuwannin jihar suna ajjiye irin wadannan mata magungunan, inda basa jirasu a cikin kanta inda ana yawan ganin matan aure da yan mata a Kofar Kwaya,Kofar Marusa,sabon gari,kofar kaura,kofar durbi da kuma blue house da misalin karfe 9:00pm har zuwa wayewar gari inda suke hada wadannan magunguna a cikin abin shan su.

Yayin da wadanda bazasu iya zuwa wajen ba suke aika yara su siyo musu inda masu siyarwa suke fara saba'ar tasu daga karfe 6:00pm zuwa 9:00pm.

DUBA WANNAN: Don Allah kada ku bar makiyaya suyi kiwo a jiharmu - Ortom ga Sarakunansa

Matan aure masu wannan dabi'a sun bayyana cewa suna shan wadannan magunguna ne dansu gamsar da mazajen su .

Yayin da wasu kuma sukace suna yin wannan Abu ne dansu kore damuwar da suke ciki.

A shekarar data gabata tsakanin watan Junairu zuwa watan March an kama masu wannan sana'ar 186 da kuma babbar mota dake dauke da kwalaben magungunan 24,000.

Da take tofa albarkacin bakin ta matar gwamnan jihar tayi kira ga shugabannin addini dasu bada tasu gudummawar wajen kawo karshen wannan dabi'a a cikin al'umma.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel