Shugaban Bankin Duniya yayi mubabus na bagatatan babu dalili

Shugaban Bankin Duniya yayi mubabus na bagatatan babu dalili

- Sai a 2022 zai gama wa'adin mulkinsa

- Ya sanya hannu a takardar ritaya a jiya

- Albashinsa ya kusa biliyan daya ta naira a wata

Shugaban Bankin Duniya yayi mubabus na bagatatan babu dalili

Shugaban Bankin Duniya yayi mubabus na bagatatan babu dalili
Source: Depositphotos

Jim Yong Kim, shugaban babban bankin duniya, yayi murabus a jiya litinin, bagatatan bayan wa'adin aikinsa sai a 2022 ne zai kare.

A takardar da ya rattabawa hannu, yace daga watan gobe, ya gama aikinsa na bankin duniya, sai dai a nemo wani a bashi, shi kam baya yi.

Albashin kujerar tasa dai, yafi naira biliyan daya in aka juya daga dala, amma tahalikin yace baya so ya gaji, a kai kasuwa.

DUBA WANNAN: A bana, yansanda zasu fara kama masu satar banten mata da laifin kokarin kisan kai

Aikin bankin duniya dai, shine fidda tsare-tsare da za'a sanya wa bankunan duniya na kasashe, yadda zasu tafiyar da hada-hadar kudi.

Bankin ke fadin yadda tattalin arzikin kasashen da duniya yake, da ma hasashen ko wacce kasa ce zata mike ko zata durkushe, bankin na kuma tallafawa kasashe masu tasowa.

Shekarar Kim dai 59, kuma ya shafe shekaru 6 a kan wannan kujera tasa. Dan asalin Koriya, ana sa rai ko dai rashin lafiya ko wasu bukatu na manyan kasashe ne suka tilasta masa sauka.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel