Sojoji za su kaddamar da atisayen Rawar Gansheka III a jihar Kebbi

Sojoji za su kaddamar da atisayen Rawar Gansheka III a jihar Kebbi

A ranar Talata 3 ga watan Janairun 2019 ne za ta kaddamar da atisayen 'Operation Python Dance III' a jihar Kebbi da ke Arewa maso yammacin Najeriya a cewar shugaban hafsin sojojin Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai.

A yayin da ya bayar da wannan sanarwar a jihar Sokoto, Buratai ya ce barayin shanu da 'yan ta'adda suna yiwa al'ummar yankin barazana.

"Barayin shanu da 'yan ta'adda sunyi sanadiyar rasuwar mutane da dama a yankin Arewa maso yamma, dole a taka musu birki."

Sojoji za su kaddamar da atisayen Rawar Gansheka III a jihar Kebbi

Sojoji za su kaddamar da atisayen Rawar Gansheka III a jihar Kebbi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Fallasa : Dan Boko Haram ya tona asirin yadda suke kai harin bam din Nyanya

Shugaban sojin ya ce ya yi imanin dakarun sojin Najeriya za su iya kawo karshen kashe-kashen sai dai duk da hakan ya ce hukumar sojin za ta cigaba da sake bawa jami'an ta horo lokaci zuwa lokaci.

A cewar Buratai, horo shine ke tabbatar da kwarewa a aiki saboda haka rundunar sojin Najeriya ta ke mayar da hankali a kan bawa dakarun ta horo.

Ya kuma yi kira ga dakarun sojojin su kyautata alakarsu da al'umma farar hula da ke yankin a yayin gudanar da atisayen na Operation Python Dance 3 a yankin na Arewa maso yammacin Najeriya.

Buratai ya kuma ja kunnen sojojin su san inda iyakarsu ta ke a yayin gudanar da atisayen da Operation Python Dance 3 saboda gujewa fadawa tarkon makiya a yayin da suke kokarin tabbatar ta tsaro a kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel