Dalilin da yasa na jawo mata ta harkar fina-finan Hausa - Jarumi Haruna Talle Maifata

Dalilin da yasa na jawo mata ta harkar fina-finan Hausa - Jarumi Haruna Talle Maifata

Haruna Talle Maifata, jarumi kuma babban darektan kamfanin shirya fina-finai na Maifata Movies, haifaffen garin Jos, jihar Filato ya bayyana matukar sha'awar sa ga sana'ar sa da ta kai shi ga jawo matar sa cikinta.

Yayin wata hira da jaridar Daily Trust, Maifata ya ce ya shiga harkar fim ne saboda sha'awar sa ga fina-finai musamman yadda take daga sunan mutum mayar da shi fitacce a cikin al'umma.

Da yake amsa tambaya a kan ko yana fuskantar kalubale tsakaninsa da matar sa a kan harkokin sana'ar sa, Maifata ya amsa da cewar akwai jituwa, yarda da fahimtar juna tsakaninsa da matar sa.

Dalilin da yasa na jawo mata ta harkar fina-finan Hausa - Jarumi Haruna Talle Maifata

Haruna Talle Maifata da Ali Nuhu
Source: Facebook

"Bari na fada maka wani abu; gidana babba ne da dakuna da yawa, wani lokacin a nan nake saukar jarumai mata idan a Jos nake shirya fim.

DUBA WANNAN: Zabe: Ganduje ya yiwa Aisha albishir mai dadi yayin kamfen din Buhari a Kano, hotuna

"Mata ta bata taba yin korafi da hakan ba, hasali ma ita ce ke dafa masu abinci. Akwai fahimtar juna tsakanina da mata ta, ta yarda da ni kuma ta san ba zan iya cin amarta ba.

"Bari ma na fada da baki na cewar nine na jawo mata ta cikin harkar fim; na bata kudin da ta dauki nauyin shirya fina-finai har guda biyu kuma na kawo ta Kannywood ne domin nuna mata irin ribar da ake samu a harkar sannan ta san babu wani abu da nake boye mata," kamar yadda jarumin ya fada a cikin hirar tasa da Daily Trust.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel