Buhari: PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina

Buhari: PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina

- A yau, Lahadi, ne jam'iyyar adawa ta PDP tayi wani taron gangami da ya matukar bawa jama'a mamaki.

- PDP ta shirya taron ne domin motsa jam'iyya da raba tuta ga 'yan takararta dake fadin jihar

- Taron ya samu halartar manya da kananun 'ya'yan jam'iyyar PDP daga lungu da sakon jihar ta Katsina

A yayin da ya rage saura kwanaki a fara zabukan shekarar 2019, jam'iyyar adawa ta PDP ta gudanar da wani taron gangami a jihar Katsina da ya matukar bawa jama'a mamaki.

PDP ta shirya taron ne don motsa jam'iyya da kuma raba tuta ga 'yan takarar kujeru daban-daban dake fadin jihar.

Taron gangamin ya bayar da mamaki musamman ganin cewar jam'iyyar APC ce ke mulki a jihar Katsina sannan kuma shugaba Buhari dan asalin jihar ne.

Buhari: PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina

PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina
Source: Facebook

Buhari: PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina

PDP tayi taro a jihar Katsina
Source: Facebook

Buhari: PDP tayi taron ban mamaki a jihar Katsina

Taron PDP a jihar Katsina
Source: Facebook

A wani labarin Legit.ng daga jihar ta Katsina, kun ji cewar a ranar Laraba da ta gabata ne gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sanar da cewa 'yan ta'adda sun mamaye sassa da dama na jihar a wurin taron gaggawa na masu ruwa tsaki a fanin tsaro inda ya ce shi da mutanen jihar na cikin hadari.

DUBA WANNAN: Zabe: Ganduje ya yiwa Aisha albishir mai dadi yayin kamfen din Buhari a Kano, hotuna

A yayin da ya ke yiwa manema labarai bayanin wasu abubuwan da aka tattauwa wurin taron, sakataren gwamnatin jihar, Fr. Mustapha Mohammed Inuwa ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar ba za ayi zabe a kananan hukumomi 8 ba muddin ba a dauki mataki ba, kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Kananan hukumomin da ya ce 'yan ta'adda da barayin shanu sun mamaye a jihar sun hada da Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume, Kankara da wasu sassan Kafur wadda itace karamar hukumar da gwamna ya fito daga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel