Kungiyar NANS ta musanya cewa ta karbi Miliyoyi a hannun Shugaban kasa

Kungiyar NANS ta musanya cewa ta karbi Miliyoyi a hannun Shugaban kasa

Kwanan nan ne rade-radi su ka fara yawo cewa Kungiyar ‘Daliban Najeriya watau NANS sun karbi makudan kudi har Naira Miliyan 150 a lokacin da su ka kai ziyara zuwa fadar shugaban kasa a Aso Villa.

Kungiyar NANS ta musanya cewa ta karbi Miliyoyi a hannun Shugaban kasa
ASUU tace Kungiyar NANS ta karbi kudi daga hannun Buhari a Aso Villa
Asali: Twitter

Kungiyar ta NANS tayi watsi da wannan magana inda tace babu kanshin gaskiya a rade-radin da Malaman jami’a na kungiyar ASUU su ke yadawa. ASUU ce ta ce ‘Daliban kasar sun karbi cin hanci daga hannun shugaban kasa.

‘Daliban kasar da ke karkashin lemar NANS, sun bayyana cewa ba a san shugaba Muhammadu Buhari da bada cin hanci da rashawa ba. Kungiyar tace kowa ya san cewa babu yadda za ayi Buhari ya ba wasu kudi haka nan a banza.

KU KARANTA: Za a kara ne a zaben 2019 tsakanin Buhari da Barayin Najeriya

Kungiyar ta ‘Daliban kasar nan tayi wannan jawabi ne ta bakin jami’in ta wanda ke hulda da jama’a watau Adeyemi Amoo. Amoo yayi kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ASUU ta ke yin a cewa an ba su kudi Naira miliyan 150.

Mista Adeyemi Amoo yace NANS tana kokarin kare muradun ‘daliban Najeriya ne kamar yadda aka san ta, inda ya bayyana irin kokarin da wannan kungiya ta ke yi wajen ganin an dawo da martabar ilmi tun ba yau ba a fadin kasar.

Kungiyar ta ‘Daliban Najeriya ta nuna cewa babu wanda ya isa ya saye su da kudi, domin kuwa gwagwarmayar da su ke yi, ba ita ba ce hanyar neman abincin su. A karshen kungiyar ta nemi ASUU ta janye yajin aikin da ta ke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng