Furucin nuna kiyayya na barazana da rashin zaman lafiya - Sarkin Zuru

Furucin nuna kiyayya na barazana da rashin zaman lafiya - Sarkin Zuru

Mai Martaba sarkin Zuru, Manjo Janar Muhammad Sani Sami Gomo II mai ritaya, ya yi kira ga dukkanin al'ummar fadar sa da kuma daukacin al'ummar jihar Kebbi, akan kauracewa furuci da kalaman na nuna kiyayya.

Furucin nuna kiyayya na barazana da rashin zaman lafiya - Sarkin Zuru
Furucin nuna kiyayya na barazana da rashin zaman lafiya - Sarkin Zuru
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Mai martaba ya ce yaduwar zantuka da kalaman nuna kiyayya na da tasirin gaske wajen haddasa barazana ta tayar da zaune gami da tarzoma a tsakankanin al'umma.

Alhaji Shehu Muhammad Bandi, Dagacin garin Rikoto, shine ya wakilci mai Martaba yayin wani taron wayar da kan al'umma da aka gudanar kan illolin yada zantuka da kalamai na nuna kiyayya.

A yayin taron wanda cibiyar yaki da furucin nuna kiyayya ta dauki nauyin gudanarwa tare da hadin gwiwar fadar Zuru, Alhaji Shehu ya bayyana cewa, ba bu ci gaba ga kowace al'umma matukar ba bu wadataccen zaman lafiya a cikin ta.

KARANTA KUMA: Najeriya ce a mataki na 110 cikin jerin kasashen duniya mafi kyawun kasuwanci - Forbes

Cikin zayyana nasa jawaban, kwamishinan yada labarai na jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Gado, Suleiman, ya yabawa fadar mai martaba sarkin Zuru sakamakon tsayuwar dakan ta wajen hada kan al'umma domin tunkarar al'amurra ma su nasaba da ci gaban kasa.

Ya jaddada yadda zaman lafiya ba za ya taba gushewa ba kan kasancewa ginshinki da kuma tubali na ci gaban kowace al'umma. Ya kuma yi kira kan dabbaka dabi'a ta hakuri da kuma juriya yayin rayuwa a zamantakewa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng