A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai

A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai

- Sama da yan Najeriya miliyan 7 suka bar gidajen su sakamakon ta'addancin Boko Haram

- Kashi 80 cikin dari na yan gudun hijirar mata ne kananan yara

- Cibiyar taimakon tayi kasafin dala miliyan 847.7 don taimaka musu

A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai
A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai
Asali: UGC

Sama da yan Najeriya miliyan 7 ne suka bar gidajen su kuma suka bukatar taimakon mutane sakamakon hare haren yan ta'addan Boko ya arewa maso gabas din Najeriya.

An bayyana rahoton ne wanda ofishin shugaban taimakon mutane na majalisar dinki duniya, OCHA, a yayin shirin taimakon rayuka na gaggawa ga inda matsalar tafi kazanta.

"A 2019, anyi kiyasin cewa mutane miliyan 7.1 ne ke bukatar taimako a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda kashi 80 cikin dari ya kunshi mata da yara," rahoton ya bayyana.

Amma cikin mutane miliyan 7.1 da ke bukatar taimako, "Miliyan 6.2 ne zasu samu taimakon, wanda ke da kashi 87 na cikin wadanda ke da bukatar, idan aka danganta su da kashi 79 da aka so yi a 2018."

Cibiyar tayi kasafin kusan dala miliyan 847.7 don magance bukatun gaggawa a 2019."

Boko Haram da ta kasu kashi biyu- kashi daya masu bin dokokin musulunci da kashi na biyu masu bin Abubakar Shekau- suna ta yada munanan manufofin su a yankin arewa maso gabas na Najeriya a cikin kusan shekaru goma.

Cigaba da kai hare hare a arewa maso gabas da kuma sojin kasar ya zama ajalin dubban mutane da Rundunar soji, fyade da garkuwa da mutane da sauran su.

A watan Fabrairu 2018, yan ta'addan sun kai hari a wata makaranta a Dapchi, jihar Yobe, inda suka sace yammata 105, kamar yanda ya faru a watan Afirilu 2014 a garin Chibok da aka kwashe yammata 200.

DUBA WANNAN: Matsaloli da dukan yara ke jawowa a kwakwalwarsu in sun girma

Kusan watannin uku bayan sace yammatan, mata ma'aikatan lafiya uku aka sace yayin da yan Boko Haram din suka kai hari a kauyen Rann, a Jihar Borno. A wannan harin ne wasu ma'aikatan lafiya guda uku da sojoji 18 suka rasa rayukan su.

Duk da mace mace ta bangaren ta'addanci ya ragu da kashi 16 cikin dari a 2017, Najeriya na cikin jerin kasashe biyar da ta'addanci yayi ma illa a kiyasin ta'addanci na duniya na shekarar 2018.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel