Hasashe: Yadda kabilu, addinai da bangarorin Najeriya zasu yi zaben 2019

Hasashe: Yadda kabilu, addinai da bangarorin Najeriya zasu yi zaben 2019

- Bode George ya taka wa Tinubu birki

- Uban tafiya a yankin Yarabawa na bangaren PDP ya fadi

- Ana sa rai Yarabawa Buhari zasu yi

'Atiku ne zabin kabilar Yorubawa ba shugaba Buhari ba'
'Atiku ne zabin kabilar Yorubawa ba shugaba Buhari ba'
Asali: UGC

Siyasar Najeriya dai ta kabilanci da bangaranci ce, inda kowanne yanki ke neman ma jama'arsa mafita, ko ta halin kaka.

Hira da aka yi da Bode George, dattijon kabilar Yarabawa, kuma tsohon abokin Obasanjo, wanda yayi zaman kurkuku bayan yayi shugaban Ports Authority inda ya bada kwangiloli ba bisa ka'ida ba, yace kabilarsu Atiku zasu yi.

Wannan furuci nasa yasa masana fashin bakin siyasa suka sake waiwaye kan yadda kabilu, bangarori da addinan Najeriya zasu yi zabe a wannan karon.

DUBA WANNAN: Wayar N750,000 da Apple tayi sun fara kamawa da wuta kamar yadda na Samsung suka yi a baya

Su dai kabilun yarabawan hankullansu sun kasu, akwai Afenifere, akwai OPC akwai ma kananan kabilu dake yankin wadanda suke da nasu hangen.

Ana sa rai dai, Igbo zasu yi PDP, yankin su GEJ watau Neja Delta ma haka, Yarabawa zasu kasu biyu, amma mafi yawansu Buhari zasu yi, Arewa maso yamma ta Buhari ce, ta gabas ma haka, tsakiyar Najeriya kuwa, sun kasu, kirista PDP, musulman kuwa APC.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel