2019: Kyautan motoci 40 da Ribadu ya baiwa Buhari ya bar baya da kura a cikin gidansa

2019: Kyautan motoci 40 da Ribadu ya baiwa Buhari ya bar baya da kura a cikin gidansa

Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana manufarsa ta ganin ya bada gudunmuwa wajen ta zarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019, inda har ya bada kyautan motoci arba’in.

A yayin bikin kaddamar da motocin daya gudana a ofishin yakin neman zaben Nuhu Ribadu dake garin Yola, Ribadu ya bayyana cewa za’ayi amfani da motocin ne wajen tattara kawunan jama’an jahar Adamawa don su zabi Buhari.

KU KARANTA; Dokar hana kiwo: Gwamnati ta mayar da shanu 187 da ta kwace ga makiyaya a Benuwe

2019: Kyautan motoci 40 da Ribadu ya baiwa Buhari ya bar baya da kura a cikin gidansa
Motocin
Asali: Twitter

Ribadu yace "Jahar Adamawa ta Buhari ce dari bisa dari, don haka zamu yi aiki tukuru don ganin shugaba Buhari ya zarce akan kujerarsa, ta haka ne kadai zai karasa ayyukan alherin daya fara, shi yasa muka yanke shawarar amfani da duk abinda muka mallaka don cimma manufa.”

Sai dai yayin da Ribadu ke bugun kirji kan kokarin da yake yin a ganin Buhari ya kai labara a zaben 2019, su kuwa wasu yayan kungiyar yakin neman zaben Nuhu Ribadu a takarar da yayi ta gwamnan jahar Adamawa, kuma jigogi a tafiyar, sun nuna ba’a tare da maganganun da yayi.

Wadannan jigogin yan siyasa sun nesanta kansu da manufar Nuhu Ribadu na cewa shugaban kasa Buhari kadai zasu yi ma yakin neman zabe, inda suka ce da fari kungiyarsu ta yanke shawarar mara ma duk wani dan takarar APC baya a jahar Adamawa ne, don haka ba zasu fasa ba.

Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan korafi da yan gagga gagga yan siyasan cikin gidan Nuhu Ribadu ne ya sanya suka kaurace ma taron kaddamar da ofishin yakin neman zaben da kuma rabon motocin, kamar yadda shugabansu Yusuf Danumma ya bayyana.

“Duba da tarukan da kungiyar yakin neman zaben Nuhu Ribadu ta gudanar, an yanke shawarar mara ma duk wani dan takarar jam’iyyar APC baya a jahar Adamawa, tare da taya shi yakin neman zabe, ba wai Buhari kadai ba.” Inji shi.

Shima sakataren shirye shirye na APC ta jahar Adamawa, Ahmed Lawan ya bayyana manufofin Nuhu Ribadu a matsayin shirin yi ma jam’iyyar APC a jahar Adamawa zagon kasa da kuma siyasar Angulu da kan zabo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng