Gwamnan Zamfara na rabon kudi ga Sojojin dake aikin dawo da zaman lafiya jihar

Gwamnan Zamfara na rabon kudi ga Sojojin dake aikin dawo da zaman lafiya jihar

- Gwamnatin jihar zamfara ta bawa sojojin da suka samu rauni Naira miliyan goma

- Sun samu raunin ne yayin da suka kai samame a dajin Dunburum dake karamar hukumar Zurmi

- Gwamnatin jihar ta jinjinawa kokarin sojojin da jami'an tsaro a jihar

Gwamnan Zamfara na rabon kudi ga Sojojin dake aikin dawo da zaman lafiya jihar
Gwamnan Zamfara na rabon kudi ga Sojojin dake aikin dawo da zaman lafiya jihar
Asali: Facebook

A jiya ne gwamnatin jihar Zamfara ta ba wa sojoji 10 da suka ji rauni kuma suke kwance a asibitin jihar kyautar Naira miliyan 5.

Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa sojojin sun samu rauni ne a samamen da suka kai wa yan ta'adda a dajin Dunburum dake karamar hukumar Zurmi ta jihar.

Samamen da ya faru a 28 ga watan Disamba yayi sanadiyar raunukany da sojojin suka samu da sojojin jamhuriyar Nijar.

Kakakin majalisar jihar, Alhaji Sanusi Rikiji ne ya mika kyautar ga sojojin, yace gwamnatin jihar ta bada ne don kyautatawa da tallafawa iyalan sojojin.

DUBA WANNAN: 1-1-2019: A yau ne Najeriya zata farlanta aiki da tsarin NIN a kan kowacce hada-hada

"A madadin gwamna Abdulaziz Yari, Ina mika kyautar Naira N500,000 ga kowanne cikin sojoji 10 da suka samu raunika suke kwance a asibiti."

"A yanzu haka mun riga mun tura kwamandan sojojin Zurmi, Kaftin Danjuma zuwa asibitin kasa dake Abuja don cigaba da magani," inji shi.

Rikiji wanda shine shugaban kwamitin gwamnatin ta saukakawa tare da duba barnar harin yan ta'adda a jihar, ya jinjinawa kokarin sojojin da sauran jami'an tsaro gurin yaki da yan ta'addan.

Ya roki mutane dasu dinga addu'a don kawo karshen hare haren da kuma bada goyon baya ga jami'an tsaro ta hanyar basu duk bayanin da ya danganci tsaro.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel