Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida

Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida

- Nonon uwa shine mafi ingancin abincin da jariri zai ci

- Nonon uwa na canzawa da watannin da jariri yayi a duniya

- Yawan ruwan nono na danganta da jaririn da mace ke goyo

Shi dai nonon uwa fin rabinsa ruwa ne, kuma ya ishi yaron, tunda cikin jariri karami ne, ruwan zai mamaye dan wurin da ya rage sinadaran dake nonon su zauna, aiki da hankali yafi rufa ido.

Duk da wasu na adawa da kin baiwa jarirai ruwa na tsawon watanni shida, bincike ya nuna wadanda bassu bada ruwan sai nono zalla 'ya'yansu suka fi kwakwalwa nasu suyi ta qere-qere namu suna gararamba a tituna.

Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida
Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida
Asali: UGC

Nonon uwa na da amfani. Ana shayarda jarirai a watanni shida na farkon rayuwar su da shi kadai kuma akwai dalilan da yasa ya zamo mafi ingantaccen abincin jarirai.

Binciken shekaru yasa an gano komai dangane da Nono cewa yafi abinci inganci. A mutane da sauran manyan dabbobi, masu bincike sun gano cewa abinda nono ya kunsa ya danganta ne da jaririn mace ne ko namiji da kuma watannin jaririn a duniya.

Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida
Dalilin da yasa ake so ku baiwa jarirai nono-zalla har wata shida
Asali: UGC

Dr Sylvester Igbedioh, mai bada shawarar fasaha a IYCF yace nono abinci ne mai matukar amfani ga lafiyar yara.

Kamar yadda yace, "Yana samar da sinadaran Vitamins, minerals da kuma kara garkuwa ga jikin yara domin girman su tare da kare lafiyarsu har zuwa shekaru biyu ko fiye da hakan na rayuwar su."

DUBA WANNAN: Ajandar Boko Haram: Ashe wai suna so su kwaci Damasak, Monguno da Abadam cikin makonnin nan ne

"Nono na da lafiya: baya bukatar a dafa shi sannan ci kuma ana iya samun shi ko a kazantaccen muhalli da ruwa mara kyau. Nono yana sa lafiyar kwakwalwa, sa'ar karatu mai yawa da kuma kariya daga cutar ciwon sukari."

Abun mamaki kuma shine sinadarydake cikin nono kan canza a yayin da jariri ke kara girma zuwa sinadaran da jikin shi yake bukata. Wannan ne yasa nono yafi kowanne abincin da za'a ba jariri inganci.

A misali, macen dake goyon mace tana samar da nono mai inganci da kuma yawa don yaro namiji.

Bugu da kari, sanuwa kan samar da nono mai yawa idan tana dauke da cikin mace fiye da idan tana dauke da namiji.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng