Matsaloli da dukan yara ke jawowa a kwakwalwarsu in sun girma

Matsaloli da dukan yara ke jawowa a kwakwalwarsu in sun girma

- Kwararru sun bayyana cewa dukan yara a matsayin horo yana iya sanya su cikin wani hali

- Yara suma mutane ne kamar kowa yafi kamata ayi musu magana sama da a dukesu

- Duka yana fahimtar da wasu yaran cewa sunyi ba daidai ba yayin da wasu yaran kuma basa ganin hakan

Matsaloli da dukan yara ke jawowa a kwakwalwarsu in sun girma

Matsaloli da dukan yara ke jawowa a kwakwalwarsu in sun girma
Source: UGC

Dabi'ar dukan yara a duk sanda sukayi laifi ba abune mai kyau ba.

Kar ku daki yara a lokacin da kuke kokarin nuna musu sunyi ba daidai ba,idan kuma zakayi dukan karkayi shi a lokacin da kake cikin fushi kuma ba tare da daukan wani abun duka ba kamar takalmi ko belt.

Bincike ya bayyana cewa yaran da ake dukansu suna tashi da wata dabi'a sannan kuma basu da wahalar kamuwa da ciwon hauka.

DUBA WANNAN: PDP na adawa da yadda aka sako sojoji daga barikoki jihoho don 'Operation Rawar Macijiya-Kaasa

Yara suma mutane ne kamar kowa sunfi bukatar ayi musu magana sama da a dakesu saboda bazasu fahimci dalilin dukan ba wannan yake janyowa su zama masu taurin kai.cewar Dr Adeyinka Labaeka likita a bangaren yara a asibitin University din Ibadan (UCH) jihar Oyo.

Duk da cewa iyaye suna da damar hukunta yara a bisa wani laifi da suka aikata amma akwai horon da bai kamata ayiwa yaro shi ba.

A bangaren Dr Abdulmalik kuma yace" Wasu yaran idan aka dakesu suna fahimtar cewa sunyi ba daidai ba yayin da wasu kuma basa fahimtar hakan suna ganin kawai idan anyi maka abinda bakaso ne kake duka".

Ya kara da cewa kamar dukan da zai janyo yaro yaji rauni yana zanyo masa cutarwa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel