Fashin Offa: Ka daina rawa a kan kabarin mamata - Lai Mohammed ya karyata Saraki

Fashin Offa: Ka daina rawa a kan kabarin mamata - Lai Mohammed ya karyata Saraki

A cigaba da zazzafar adawa dake tsakaninsu, ministan yada labarai na kasa, Lai Mohammed, ya karyata ikirarin shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a kan cewar ya bayar da gudunmawa miliyan N5m ga wadanda suka yi asara yayin fashin da aka yi a ranar 5 ga watan Afrilu a garin Offa, jihar Kwara.

A wani jawabi da Ministan ya fitar yau, Litinin, a Legas ya yiwa Saraki hudubar ya "daina rawa a kan kabarin jama'ar da suka rasa ransu" yayin fashin garin na Offa.

Jawabin, mai dauke da sa hannun Segun Adeyemi, mai bayar da shawara na musamman ga ministan, an raba shi ga manema labarai a Abuja.

"Bai bayar da wani tallafi ba! Miliyan N10m da yake magana a kai, ya bayar ne lokacin da aka yi gobara a kasuwar Ilorin, ba garin Offa ba.

"Lokacin da ya ziyarci garin Offa bayan fashi da aka yi, be bayar da ko sisi ba. Na kalubalence shi ya gabatar da hujjar cewar ya bayar da wani tallafi," a cewar ministan.

Fashin Offa: Ka daina rawa a kan kabarin mamata - Lai Mohammed ya karyata Saraki

Lai Mohammed ya karyata Saraki
Source: Depositphotos

Mohammed ya gargadi Saraki da ya daina saka siyasa a cikin iftila'in da ya fadawa jama'ar garin Offa.

Kazalika ya zargi Saraki da yin furucin bayar da tallafin miliyan N10m lokacin da ya je yiwa jama'ar garin Offa jaje yayin wata hira da shi.

DUBA WANNAN: 2019: Atiku na kulle-kullen shigowa da makudan kudi - BMO

Mohammed ya kara da cewa, a cikin hirar, Saraki ya yi ikirarin cewar ya bayar da tallafin miliyan N10m, adadin da ya wuce na kudi miliyan N7m da 'yan fashin suka sata daga ma'ajiyar bankuna.

"Saraki ya yi watsi da shi da duk hudubar da muka yi a kan saka siyasa a cikin batun fashin, hakan ya sa tilas na fito nayi Alla-wadai da duk wani yunkuri na yin kaskantar da ran mutum ta hanyar amfani da Naira da Kobo," a cewar Mohammed.

Ministan ya kara da cewa mutanen jihar Kwara sun san su waye makiyansu kuma zasu nuna fushinsu da kuri'ar su nan bada dadewa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel