Wasu sabbin sojoji sun tarwatsa taron biki, sun zane jama'a
- Wasu sabbin sojoji da suka kammala karbar horo a makarantar soji (NDA) sun wahalar da matafiya a hanyar Mararaba zuwa Keffi
- Sabbin sojojin Basu bayar da wani dalili na aikata abinda suka yi ba
- Jama'a, musamman a dandalin sada zumunta, sun yi Alla-wadai da yadda sabbin sojoji suka wulakanta mutane
Wasu sabbin kananan sojoji dake karbar horo a makarantar sojoji (NDA) sun yi watsi da ka'idojin aiki inda suka datse sashen hanyar Mararaba zuwa Keffi tare da wahalar da matafiya.
A wani faifan bidiyo dake yawo a dandalin sada zumunta, an ga daya daga cikin sojojin na zagin jama'a tare da fada masu dole su yi abinda yake so.
Matasan basu tsaya iya nan ba saida suka shiga wurin wani biki, ba tare da an gayyace ba, suka tarwatsa jama'a.
Bayan wanda ya shirya bikin yayi korafi a kan yadda suka shigo wurin taronsa suna cin mutuncin jama'a, sai suka umarce shi ya rike kunnensa ya fara tsallen kwado.
A yayin da mutumin ya nuna alamun gajiya da tsallen kwadon ne, sai sojojin suka umarce shi ya kara sauri tare da zaginsa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta gani a faifan bidiyon.
Wata majiya ta shaida mana cewar irin wannan halayya ba bakuwa ba ce a tsakanin sabbin kananan sojoji domin har wani lakani 'plumming 101' ake yiwa hakan.
DUBA WANNAN: Hisbah ta kama wani saurayi da ya yiwa 'yan mata 3 a gida daya fyade
Faifan bidiyon ya jawo barkewar cece-kuce da tofin ala-tsine daga dubban 'yan Najeriya a dandalin sada zumunta.
Sai dai duk da fushin da jama'a suka nuna, Chibuisi Ojukwu, wani soja gaba da sabbin sojojin, ya yabe su tare da fadin cewar yin hakan ya halasta a tsarin rayuwar sabbin sojoji.
Kazalika wani sojan, Sadiq Abubakar, ya ce sabbin sojojin sun yi daidai.
Sai dai Manjo Abubakar Abdullahi, kakakin NDA ya ce ya kalli faifan bidiyon kuma zasu gudanar da bincike.
Ya kara da cewa rundunar soji ba zata yarda da irin halayyar da yaran suka nuna ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng