Jihar Kano ta samu Farfesa na farko a kimiyyar na'ura mai kwakwalwa

Jihar Kano ta samu Farfesa na farko a kimiyyar na'ura mai kwakwalwa

A ranar Asabar, 29 ga watan Disamba, ne 'yan uwa da abokan arziki suka shirya liyafar taya Ahmed Baita Garko murnar zama Farfesa na farko a kimiyyar na'ura mai kwakwalwa daga jihar Kano.

Ahmed Baita Garko, dan asalin karamar hukumar Garko ta jihar Kano, ya ce babban kalubalen da yake fuskanta a matsayinsa na Farfesa a kimiyyar na'ura mai kwakwalwa, shine yadda zai bawa dalibansa ilimin da yake da shi.

Da yake jawabi yayin bikin taya shi murnar da aka yi a garin Garko, Ahmed ya ce zama Farfesa a bangaren kimiyyar na'ura mai kwakwalwa, ba abu ne mai sauki ba.

Jihar Kano ta samu Farfesa na farko a kimiyyar na'ura mai kwakwalwa
Farfesa Ahmed Baita Garko
Asali: Facebook

Ya kara da cewa zai tabbatar al'ummar mahaifar sa sun karu daga ilimin da yake da shi ta hanyar kafa wata cibiya da zata ke bayar da horo a bangaren sarrafa na'ura mai kwakwalwa.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya halarci bikin gargajiya daga shi sai dan kamfai, hotuna

A cewar sa, cibiyar zata bawa matasa a jihohin Jigawa da Kano damar samun ilimi a kan kimiyyar na'ura mai kwakwalwa da sarrafa ta.

An bawa Ahmed Baita lakanin Farfesa ne a shekarar da ta gabata a jami'ar gwamnatin tarayya dake garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Farfesa Ahmed ya mika sakon godiya ga 'yan uwansa da abokai da suka shirya masa liyafar taya shi murna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel