Dakarun Soji sun yi sabon shugaba bayan hare-haren Boko Haram

Dakarun Soji sun yi sabon shugaba bayan hare-haren Boko Haram

Mun samu labari cewa an sauya wanda ke jagorantar wasu Dakarun sojojin Bataliya ta 7 na Najeriya. Hakan na zuwa ne yayin da ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka ci galaba kan sojojin da ke Garin Baga.

Dakarun Soji sun yi sabon shugaba bayan hare-haren Boko Haram
Sojoji sun karyata cewa Boko Haram sun karbe Garin Baga
Asali: UGC

Shugabannin sojin kasar sun cire Birgediya Janar A. Hassan daga mukamin sa bayan da ‘Yan Boko Haram su ka karbe Garin Baga da ke daf da tekun Chadi a Arewacin jihar Borno. Ana sa rai za a nada wani jagora kwanan nan.

Yanzu haka dai ana cigaba da bude wuta tsakanin Sojojin Najeriya da ‘Yan Boko Haram a yankin na Arewa maso Gabashin kasar nan. Rahoton da mu ke samu shi ne yanzu haka ‘Yan ta’addan sun tsare Garin Munguno da ke Borno.

Rundunar ta 7 na sojojin Najeriya wanda aka canzawa shugaba tana cikin babban bangaren Hedikwatar babban rundunar hadin-gwiwa na MNJTF. A cikin makon tsakiyar jiya ne ‘Yan ta’addan su ka kai hari har cikin Hedikwatar na MNJTF.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun karbe garuruwa 6 a cikin Jihar Borno

Daily Trust ta rahoto cewa mayakan Boko Haram da ke tare da banagren Abu Mus’ab Albarnawi sun shigo Yankin Arewacin jihar Borno ne da manyan makamai inda su ka karbe Garin Baga kuma ake cigaba da kai hare-hare a Munguno.

Sojojin kasar sun musanya cewa Boko Haram sun karbe Garin Baga, amma ta tabbata cewa yanzu ‘Yan ta’addan ke rike da Garin. Sojojin kasa da sama na Najeriya dai su na cigaba da kokari wajen fatattakar ‘Yan ta’addan daga Yankin.

Garuruwa irin su Zari, Jilli, Gudumbali, Arege, Kukawa da Metele duk su na hannun ‘Yan ta’adda. Haka kuma jama’an da ke cikin dar-dar sun hada da mutanen Garuruwan, Arge, Alagarnon, Kangarwa, Kuroskauwa, da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel