Dakarun Soji sunyi nasarar kashe mata 'yan kunan bakin wake uku
- Dakarun sojin Najeriya sunyi nasarar kashe 'yan kunar bakin wake uku a ranar Lahadi 30 ga watan Disambar 2018
- Dakarun Sojin kuma sun kwace Rocket Propelled Grenade (RPG) guda daya da rigar bam
A ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba ne Dakarun Sojin Najeriya suka kashe wasu mata uku 'yan kunan bakin wake a kauyen Kubtara da ke karamar hukumar Dikwa na Jihar Borno a yayin da suke sintiri.
Sanarwar da ta fito daga mataimakin Direktan hulda da jama'a na Rundunar Operation Lafiya Dole, Kwanel Onyema Nwachukwu a ranar Litinin ta ce sojojin sun kwace Rocket Propelled Grenade da rigar bam bayan kashe 'yan kunar bakin waken.
DUBA WANNAN: Da dumi-dumi: Boko Haram ta sake kai hari garin Buni Gari
Nwachukwu ya ce hafsin hafsoshin Najeriya, Laftanat Tukur Buratai ya yabawa dakarun sojin bisa nasarar da suka samu a kan 'yan ta'addan.
Buratai ya bukaci sojojin su cigaba da kara kwazo kuma su kasance cikin shiri a ko yaushe domin ganin sun kawar dukkan sauran 'yan ta'addan da suka rage.
A wani rahoton, hukumar Soji ta yi kira da al'umma suyi watsi da wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke haska wani soja yana korafi a kan rashin isasun kayan aiki inda su kace ba haka lamarin ya ke a yau ba.
Direktan yada labarai na Soji, Brig. Janar Sani Usman ya ce bidiyon tsoho ne kuma abubuwan tuni sun canja a halin yanzu.
"Wannan ba gaskiya bane saboda anyi bidiyon ne tun shekarar 2014 saboda haka ba shi da tasiri a yanzu.
"Muna kira da al'umma suyi watsi da wannan faifan bidiyon," inji Usman.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng