SERAP: An kai kukan Shugaba Buhari har gaban Majalisar dinkin Duniya saboda yajin ASUU

SERAP: An kai kukan Shugaba Buhari har gaban Majalisar dinkin Duniya saboda yajin ASUU

Kungiyar SERAP mai rajin kare hakkin jama’a a Najeriya tayi kira ga majalisar dinkin Duniya watau UN ta tursasawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen yajin aikin da ake yi a jami’o’in Najeriya.

SERAP: An kai karar Shugaba Buhari har gaban Majalisar dinkin Duniya saboda yajin ASUU

SERAP ta maka Buhari a gaban Majalisar dinkin Duniya
Source: UGC

Wani babban jami’in Kungiyar ta SERAP ya nemi majalisar dinkin Duniya tayi maza-maza ta matsawa shugaba Buhari ya sasanta da ‘Yan kungiyar ASUU na malaman jami’o'in Najeriya wanda har yanzu su ke ta faman yajin aiki a kasar.

Bamisope Adeyanju ya bayyana cewa rashin shawo karshen yajin aikin da ake yi a jami’o’in kasar ya sabawa wata doka ta kasashen waje da Najeriya tayi imani da ita, wanda ta ce gwamnati za ta ba kowa damar samun karatu mai nagarta.

Adeyanju ya nemi Ms. Koumbou Boly Barry da kuma Farfesa Philip Alston da ke aiki a matsayin manyan jami’o’in harkar ilmi da kare hakkin Bil Adama da kuma bangaren yaki da talauci na majalisar UN su kawowa Najeriya dauki.

KU KARANTA: An bukaci a auna kaifin hankalin Buhari da Atiku gabannin zaben 2019

SERAP ta koka da cewa idan har ASUU ta cigaba da yaji, hakan zai kawowa yaran talakawa da ke karatu a makarantun gwamnati cikas, yayin da masu hali su ke zuwa makarantun kasuwa inda ba a yajin aiki domin su samu ilmi mai nagarta,

Jami’in yace wannan banbanci da ake nunawa wajen daukar karatu ya ci karo da yarjejeniyar da Najeriya da sauran kasashe su ka shiga inda aka yarda cewa ba za a nuna wariya wajen bada ilmi ko karfafawa ‘yan kasar ta fuskar tattali ba.

An dauki kusan watanni 2 kenan ana yajin aiki a jami’o’in Najeriya. Kungiyar Malaman sun ce ba za su janye yajin aiki bar har sai gwamnatin kasar ta dabbaka yarjejeniyar da ake yi da ita a 2009 da kuma 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel