Da dumi-dumi: Boko Haram ta sake kai hari garin Buni Gari

Da dumi-dumi: Boko Haram ta sake kai hari garin Buni Gari

Mayakan Boko Haram sun kai hari a garin Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba na jihar Yobe.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan ta'addan sun shiga garin ne misalin karfe 6 na yammacin jiya Asabar inda suka rika harba bindiga sannan suka kone gidajen al'umma da dama.

Wannan shine karo na biyu da 'yan ta'addan ke kai hari a garin a cikin kwanaki 30.

Mazauna garin sun shige cikin dajin da ke kusa da garin domin su tsira da ransu. Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa sun kai harin ne a matsayin daukar fansar 'yan ta'adda biyu da kungiyar mafarautan garin suka kashe.

Da dumi-dumi: Boko Haram ta sake kai hari garin Buni Gari
Da dumi-dumi: Boko Haram ta sake kai hari garin Buni Gari
Asali: UGC

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

Baana Musti ya bayyana cewa kwanaki 10 da suka wuce, 'yan ta'adda guda hudu sun iso kauyen idan su kayi yunkurin sace wata mace guda daya da suka ce matarsu ce amma sai mafarautan suka taka musu birki.

"Mijin matan mazaunin garin ne hakan yasa mafarautan ba su kyale an tafi da ita ba. Sun kashe biyu cikin 'yan ta'addan sannan suka mika guda ga sojoji shi kuma na karshen ya tsere. Wannan lamarin ya afku ne kwanaki 20 da suka gabata," inji shi.

Wani mazaunin garin da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce sun san cewa 'yan ta'addan za su kawo farmaki a garin shi yasa mutane da dama suka gudu kafin a kawo harin.

"Mutane fiye da 2,000 sun boye a daji a halin yanzu, bamu san yadda za muyi ba. Mun ji labarin cewa har yanzu suna nan suna kone gidajen mu," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel