Boko Haram: Hukumar Soji na shirin yiwa mutanen Baga canjin matsuguni

Boko Haram: Hukumar Soji na shirin yiwa mutanen Baga canjin matsuguni

- Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da cewa za ta kwashe mutanen Baga zuwa wasu garuruwa

- Za a sauya wa mutanen matsuguni ne saboda atisayen da dakarun soji keyi a garin na Baga

- Hukumar Sojin tayi kira da al'umma su kwantar da hankulansu kuma suyi watsi da duk wani jita-jita da wasu masu neman tayar da zaune tsaye ke yadawa

A yau Lahadi ne Hukumar Sojin Najeriya ta sanar da cewa tana shirin kwashe mutanen Baga da ke jihar Borno zuwa wasu garuruwan dubba da irin atisayen da dakarun sojin su keyi a garin a cikin 'yan kwanakin nan.

Hukumar Sojin ta ce za ta gudanar da wannan aikin ne tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Borno.

Boko Haram: Za a yiwa mazauna Baga canjin matsuguni

Boko Haram: Za a yiwa mazauna Baga canjin matsuguni
Source: Twitter

A cikin yan kwanakin nan ana da bata kashi tsakanin sojojin Najeriya da mayakan kungiyar Boko Haram. A ranar Juma'a, hukumar Sojin Saman Najeriya ta sanar da cewa ta aike da jiragen yaki domin suyi ruwan bama-bamai a wasu mabuyar 'yan ta'adda.

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

A ranar Lahadi, Hukumar Soji ta fitar da sanarwa ta bakin Onyeka Nwachukwu inda ta ce wasu masu hana neman tayar da zaune tsaye suna kokarin tayar da hankulan al'umman wasu garuruwa a Borno.

Mai magana da yawun hukumar Sojin Najeriya, Sani Usman ne ya yada sanarwar a shafinsa na kafar sada zumunta na Facebook.

Wani bangare na sakon ya ce, "Mun gano cewar wasu masu neman hadasa fitina a ciki da wajen Borno suna kokarin tayar da hankulan al'umma ta hanyar tunzura mutanen garuruwan Bama, Dikwa da Monguno su bar gidajensu su koma sansanin masu gudun hijira.

"Muna kira da mazauna garuruwan nan da su zauna a gidajensu. Rundunar Operation Lafiya Dole da sauran hukumomin tsaro za suyi karin haske kan lamarin a taron kwamitin tsaro da za ayi da gwamnatin Borno a ranar Litinin 31 ga watan Disambar 2018."

Hukumar Sojin tayi kira da al'umma su kwantar da hankulansu amma ta ce Rundunar Operation Lafiya Dole da sauran hukumomin tsaro na shirin canja wa mutanen Baga matsuguni saboda atisayen da soji keyi a garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel