Sunaye: Rundunar 'yan sanda ta zare wasu manyan jami'anta daga aiki

Sunaye: Rundunar 'yan sanda ta zare wasu manyan jami'anta daga aiki

A yau, Asabar, ne rundunar 'yan sanda ta kasa ta yiwa tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Legas Fatai Owoseni, da ragowar wasu 9 ritaya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Owoseni ya kasance kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas daga Yuli na shekarar 2015 zuwa watan Satumba na shekarar 2017.

NAN ta rawaito cewar an yiwa jami'an bikin barin aiki mai kayatarwa da ya samu halartar 'yan uwa, dangi da abokan arzikin masu ritayar a garin Legas.

Babban mataimakin Sifeton 'yan sanda, Ibekwe Abdallah, wanda ya wakilci IG, Ibrahim Idris, ya yabawa jami'an bisa gudunmawar da suka bayar ga aikin dan sanda.

Sunaye: Rundunar 'yan sanda ta zare wasu manyan jami'anta daga aiki

Rundunar 'yan sanda ta zare wasu manyan jami'anta daga aiki
Source: Depositphotos

"Ina taya ku murnar kammala aiki lafiya kuma cikin nasara.

"A yayin da ku ka bar aikin dan sanda, shugaban rundunar 'yan sanda na yi maku godiya, Allah ne kadai zai iya saka maku," a kalaman Ibekwe.

DUBA WANNAN: An binne marigayi tsohon shugaban kasa Shagari a mahaifar sa, hotuna

Ragowar manyan jami'an 'yan sanda da suka yi ritayar sun hada da AIG Abdul Bube, AIG Hilda Ibifuro-Harrison, CP Agyole Abeh, CP Joseph Agaji da CP Gbemisola Akinpelu.

Ragowar sune; CP Bello Ahmed, CP Abdullahi Ibrahim, CP Bello Yahaya, CP Adekinte Ademoju, CP Wakili Maye, CP Fave Semili da CP Ahmed Magaji.

NAN ta kara da cewa jami'an 'yan sanda 55, masu mukamin AIG, kwamishinoni, mataimakan kwamishinoni da kananun mataimakinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel