PDP na adawa da yadda aka sako sojoji daga barikoki jihoho don 'Operation Rawar Macijiya-Kaasa

PDP na adawa da yadda aka sako sojoji daga barikoki jihoho don 'Operation Rawar Macijiya-Kaasa

- Sojojin Najeriya zasu bazama yankunan da ake tada kayar baya don kawar da muggai

- PDP tace lamarin yayi kama da kokarin baiwa masu zabe tsoro a jhohi

- APC take aikin dawo da zaman lafiya ne, saboda abubuwa sunzo wa kowa wuya

PDP na adawa da yadda aka sako sojoji daga barikoki jihoho don 'Operation Rawar Macijiya-Kaasa

PDP na adawa da yadda aka sako sojoji daga barikoki jihoho don 'Operation Rawar Macijiya-Kaasa
Source: Facebook

PDP Presidential Campaign Organization (PPCO), wadda ke dauke da alhakin ganin an zabi Atiku ya maye gurbin shugaba Buhari a badi May 29, ta zargi sabbin tsare-tsare da ake yi tsakanin hukumomin tsaro don kawar da barazanoni dake fuskantar kasar nan kan tsaro.

In masu karatu na kula dai, kamar muggai sun daura damarar rikita kasar nan ana dab da zabe, kashe can, kona can, ruguza can, ballo can, lamari da yasa wasu ma ke rasa imaninsu da gwamnatin Buhari ko da gaske zai iya fahimtar sabuwar Najeriya mai cike da kiki-kaka da muggai.

DUBA WANNAN: Sojin Najeriya sun baras da sabon yunkurin Boko Haram a Goniri, sun kwato manyan motocin igwa ta yaki

PDP din dai, tace, wannan shiri da soji ke yi, na mamaye tituna da dazukan wasu yankuna a kasar nan, somin tabi ne na kokarin murde zaben da shugaba Buharin ya tabbatar zai fadi warwas, shi yasa yake son amfani da soji da 'yansanda don murkushe masu jefa wa PDP kuri'u, ko ma basu tsoro.

Tabbas dai, a kasashe irin namu, ana amfani da hukumomin tsaro don murde burin talakka, ko don dora sabuwar gwamnati ko sauke ta, wannan yasa masu adawa kan iya kokarinsu su ja hankulan mutane su baza ido suga me soji ke shirin yi.

Hukumar Soji dai tace, Operation Python Dance, aiki ne na dawo da doka da oda, a yankunan da ake samun matsalar tsaro, kuma za'a yish ia gama laiya, babu ruwansa da siyasa ko jama'a.

An dai yi irin wannan shiri bara a kudu, inda aka daqile masu son ballewa daga Najeriya su kafa tasu kasar ta Bayafara, kuma yayi nasara.

Wasu kuwa daga bangaren masu adawa, na ganin ma ai ko karin albashi da shugaban kasa yayi wa 'yansanda a watan jiya wani nau'i ne na kwarapshan, musamman ganin su kadai ya ware ya kara wa, ya bar sauran ma'aikata.

Bayan haka kuma, an zargi Osinbajo da rabon kudi ana cikin kamfe na tazarce, inda Farfesan yace ai kudin N10,000 jari ne yake rabawa mata da kananan 'yan kasuwa, daga kudaden da aka kwato daga wadanda Janar Abacha ya 'adanawa 'yan Najeriya' da sunan iyalansa a Turai.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel