Kididdigar irin ayyukan da Ministan Tsaro Mansur dan-Ali yayi a cikin shekarun nan

Kididdigar irin ayyukan da Ministan Tsaro Mansur dan-Ali yayi a cikin shekarun nan

- Dan Jarida Callistus Ijeh na bin diddigin ayyukan Ministan Tsaro

- Har yanzu ana samun matsalolin tsaro a Najeriya

- Ministan ana cewa ya gaza, shi kuma bai fiye hira da manema labarai ba

Kididdigar irin ayyukan da Ministan Tsaro Mansur dan-Ali yayi a cikin shekarun nan
Kididdigar irin ayyukan da Ministan Tsaro Mansur dan-Ali yayi a cikin shekarun nan
Asali: Facebook

Bayan kashe-kashe a jiharsa ta Zamfara, manema labarai, da ma masu sanya ido kan lamarin tsaro a ciki da wajen Najeriya, na duba wai ko ma dai ministan tsaro Janar Mannir dan-Ali mai ritaya na aikinsa da ya kamata, ko kuwa dumama kujera kawai yake yi?

Kididdigar irin ayyukan da Ministan Tsaro Mansur dan-Ali yayi a cikin shekarun nan
Kididdigar irin ayyukan da Ministan Tsaro Mansur dan-Ali yayi a cikin shekarun nan
Asali: Facebook

Dan Ali dai ya shiga aikin soja na Short Service a 1894, ya kuma rike mukamai da dama, wadanda suka hada da Aikin zaunar da kasar Sudan lafiya na majalisar dinkin barakar duniya.

Yayi Kwamandar Kalejin koyon aikin sojoji ta Jaji a 2003-2005, da ma C.I, watau Cif Instructor, a 2010 a NDA.

Yazo yayi wasu ayyukan na Posting, a ma'aikatar tsaro, a matsayin mataimakin Darakta kafin yayi ritaya a 2013, ana tsaka da yakin Boko Haram a Najeriya.

DUBA WANNAN: Gaskiyar magana kan zargin wai ko iyalan Buhari ke da Etisalat da bankin Keystone

Babu dai wata kwarewa a aiki a dukkan tarihin ayyikan da Mansur dan-Ali yayi a lokutan da yake soja, inji marubucin a sharhinsa na jaridarSahara Reporters, ya kuma ce babu wani abin kuzo ku gani da yanzu yake yi a matsayin ministan tsaro na farar hula, musamman ganin irin ta'asar da ake tafkawa a jiharsa ta haihuwa watau Zamfara.

Kuma ma dai, babu wani ci gaba a yakin da ake da Boko Haram, gama ga gashi har yanzu soji na asarar rayukansu a yankunan da aka kaisu, kuma ga alama wasu wuraren ma ko zabe ba'a iya yi ba a yankunan, musamman ganin tuni babu mutane a yankunan, sun tsere sun gudo Maiduguri, Kano da Abuja.

Ana dai yawan caccakar Mansur dan Ali da Abdurrahman Dambazau ministan cikin gida kan yadda tsaro yaki samuwa bayan kuwa dasu da shugaba Buhari da Buratai duk sojoji ne.

Wannan ra'ayin marubuci Callistus Ejeh ne muka gutsuro muku...

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel