Rundunar soji ta fitar da sunayen masu neman aiki a rukunin manyan ofisoshi

Rundunar soji ta fitar da sunayen masu neman aiki a rukunin manyan ofisoshi

Hukumar soji ta fitar da jerin sunayen wadanda suka nemi aiki da rundunar soji a matsayin manyan ofisoshi (SSC) da (DSSC) na shekarar 2019. Za a fara tantance wadanda sunayensu suka fito daga ranar 4 ga watan Janairu zuwa rana 18 ga wata.

A sanarwar da hukumar sojin ta fitar a jiya, Alhamis, ta ce za a fara tantance masu neman aikin na rukunin SSC a tsohon ginin NDA dake Kawo a Kaduna yayinda na rukunin DSSC za a yi a barikin rundunar soji dake Serti Baruwa a jihar Taraba.

Tun kafin fitowar sunayen, rundunar hukumar soji ta gargadi masu neman aikin da su guji fadawa hannun shugabanta damfara yayin da suke neman aiki, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Facebook.

Kazalika ta shaida masu cewar su yi watsi da wasu lambobin waya da ake zagaya wa da su a kan cewar duk mai neman taimako wajen samun aiki a hukumar soji ya kira daya daga cikinsu.

Rundunar soji ta fitar da sunayen masu neman aiki a rukunin manyan ofisoshi
Manyan ofisoshin rundunar soji
Asali: UGC

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bugi kirjin cewar ta gurfanar da kimanin mutane 312 da ta kama a kan aikata laifukan cin hanci da rashawa a tsakanin watan Janairu da ranar 24 ga watan Disamba na shekarar 2018.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun daga ranar bajakolin wadanda suka kashe Alex Badeh

A sanarwar da ta fitar ta bakin kakakinta, Tony Orilade, EFCC ta ce ta samu gagarumar nasara idan aka kwatanta da adadin mutane 189 da ta gurfanar a shekarar 2017.

Sanarwa ta ce, "mafi muhimmanci shine kasancewar tsofin gwamnoni biyu daga cikin mutanen da muka gurfanar, wadanda yanzu haka suna gidan yari bayan kotu ta yanke masu hukunci. Akwai babban lauya, Joseph Nwobike, da hukumar EFCC ta janyo ya rasa lasisinsa na aikin lauya bayan samun sa da laifin kokarin dakile hukuncin kotu.

"Da wadannan nasarori da EFCC ta samu karkashin jagorancin Ibrahim Magu, hukumar ta tabbatar da ikirarinta na yaki da cin hanci domin inganta tsarin gudanar da gwamnati a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel