Gwamnatin tarayya ta tura karin jami'an tsaro zuwa Zamfara - Dambazau

Gwamnatin tarayya ta tura karin jami'an tsaro zuwa Zamfara - Dambazau

Ministan harkokin cikin gida, Laftanat Janar Abdulrahman Dambazau (mai murabus) ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta karo jami'an tsaro zuwa jihar Zamfara domin ganin an kawo karshen kashe-kashen mutane da asarar dukiyoyi.

Dambazau ya bayar da wannan tabbacin ne a wata sako da ta fito daga bakin mai magana da yawun sa, Osaigbovo Ehisienmen a ranar Alhamis a Abuja.

Ministan ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta'azziyarsa ga gwamnati da al'ummar jihar Zamfara bisa rasa rayyuka da dukiyoyi da akayi sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai a jihar cikin 'yan kwanakin nan.

DUBA WANNAN: Wani da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan

Gwamnatin tarayya ta tura karin jami'an tsaro zuwa Zamfara - Dambazau
Gwamnatin tarayya ta tura karin jami'an tsaro zuwa Zamfara - Dambazau
Asali: Depositphotos

Dambazau ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana matukar damuwa kan yadda har yanzu 'yan ta'addan suke cigaba da kashe-kashe a jihar.

"Muna aiki tare da gwammatin jiha domin ganin mun karo jami'an tsaro zuwa jihar," inji Dambazau.

Ehisienmen ya ce shugabanin hukumomin tsaro a jihar na Zamfara sun yiwa ministan bayanai ta yadda za a dawo da zaman lafiya a jihar tare da kiyaye amfani gona da ma'adinai na kasa a jihar.

A cewar sanarwar, mukadashin gwamnan jihar, Mr Sanusi Rikiji da sauran 'yan fadan gwamnatin jihar ne suka tarbi Dambazau yayin da ya isa jihar.

Daga baya, Ministan ya tafi fadar mai martaba sarkin Katsina Gusau, Mai martaba Dr Ibrahim Bello, Sarkin Gusau.

A yayin da ya ke fadar, Dambazau ya bawa Sarkin tabbacin cewa gwamnati tana iya kokarin ta domin ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Ya kuma ce ministan ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar da kuma hedkwatan karamar hukumar Tsafe inda masu zanga-zanga suka lalata motocci da wasu kayayaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel