Cikuna sun duri ruwa, bayan da Buhari yace zai kakkabe mugayen jihar Kwara kafin zabe

Cikuna sun duri ruwa, bayan da Buhari yace zai kakkabe mugayen jihar Kwara kafin zabe

- Anso a laqa wa Saraki hare-haren Offa na 'yan fashi

- Saraki ya karyata yana da hannu a lamarin

- Kakakin Buhari yace zasu kakkabe jihar daga muggai

Cikuna sun duri ruwa, bayan da Buhari yace zai kakkabe mugayen jihar Kwara

Cikuna sun duri ruwa, bayan da Buhari yace zai kakkabe mugayen jihar Kwara
Source: UGC

Tun bayan da 'yan fashin da suka tagayyara jihar Kwara suka zo hannu, Bukola Saraki, na uku a mulki a kasar nan, ya shiga dimuwa kan ko gwamnati na niyyar kaishi kurkuku ne ko ta halin qaqa, bayan da ya tsallake kotun CCT.

Sai da ma ya bar jam'iyyar APC, sannan aka mai da batun siyasa, inda kuma wanda ake zargi da fadin sunan na Bukola Saraki, ya mutu a hannun 'yansanda, ba'a san dalili ba.

Sai gashi kuma, kakakin shugaba Buhari, mai magana da yawun gwamnatin, yace kafin zaben 2019 zasu kakkabe dukkan wani mugu daga jihar ta Kwara.

DUBA WANNAN: A Siyasa babu dan gida, sai wanda ra'ayinku yazo daya, siyasar Kano a yau

Alhaji Lai Muhammed, ya dai ari bakin shugaba Buhari ne ya tauna albasa, lokacin da ya je garin Offa a dazu, domin bude sabon ofishin tsaro na hukumar 'yansanda mai dan-karen tsada har ta N700m, ta zamani.

'Yan garin na Ofa da ma wasu na jihar ne dai suka hada wannan kudi, don inganta tsaro, wadda ake sa rai ma ko Bukola Sarakin ne ya gina ta da sunan wasu don wanke kansa daga zargi, domin kuwa lamarin yaso bata masa siyasarsa.

Shaguben na Lai Muhammed dai, na nuni da har yanzu, ana jika kan kokarin gwamnatin APC na ganin ko dai ta kunyata Bukola Saraki, ko kuma hukuntashi in an same shi da laifi, musamman ganin ma ya sauya sheka yabi su Atiku.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel