Hotunan yadda sojoji su kayi bikin kirsimeti na bana

Hotunan yadda sojoji su kayi bikin kirsimeti na bana

Shugaban hafsin sojojin Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai tare da sauran manyan shugbanin soj sun shirya liyafar bikin kirsimeti na musamman domin dakarun sojin Najeriya na Lafiya Dole da ke aikin samar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

Anyi bikin ne a sansanin sojin Najeriya na Foward Operation Base da ke Delwa a karamar hukumar Konduga a ranar 26 ga watan Disambar 2018.

A jawabin da ya yi a wajen bikin, Buratai ya jinjinawa dakarun sojin da suka rasu a yayin yaki da ta'addancin kuma ya taya sojojin murna kan jarumtarsu.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya lissafo dalilai 3 da yasa manyan Arewa su kayi gum a kan yawaitar kashe-kashe a yankin

Shugaban hafsin sojin ya fadawa sojin cewa gwamnatin Najeriya tayi alkawarin basu dukkan goyon bayan da suke bukata domin ganin sun ci galaba a kan yaki da ta'addancin da su keyi.

Wani abin sha'awa a bikin shine yadda shugaban hafsin sojin, TY Buratai da sauran manyan shugabanin sojojin suka rabawa dakarun sojin na Operation Lafiya Dole abinci da abubuwan sha da kansu.

Wadanda suka yiwa shugaban hafsin sojin rakiya sun hada da Major General LO Adeosun, Direktan sashin tattara bayanan sirri, Major General SA Adebayo, Shugaban kasafin kudin Soji, Major General CU Agunlanna, Kwamandan Operation LAFIYA DOLE, Major General BA Akinroluyo da Brigadier General H Ahmed.

Ga hotunanan a kasa

Hotunan yadda sojoji su kayi bikin kirsimeti na bana

Hotunan yadda sojoji su kayi bikin kirsimeti na bana
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel