PDP tayi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a Yobe da Zamfara

PDP tayi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a Yobe da Zamfara

Babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, ta fito ta tofa albarkacin bakin ta bayan hare-haren da ‘yan Boko Haram su ka kai a cikin Jihar Yobe da kuma kashe mutane da aka yi a Garin Zamfara kwanan nan.

PDP tayi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a Yobe da Zamfara
Kola Ologbondiyan ya nemi Buhari ya sake sabon lale a gidan Soja
Asali: Twitter

A cikin makon da ya gabata, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe jamia’n tsaro a Garin Kukareta da ke cikin Jihar Yobe. Bayan nan kuma wasu tsageru da su ka fitini mutanen Jihar Zamfara sun sake kai hari a wasu Garuruwan Jihar.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta fitar da jawabi tana cewa wannan munanan hare-haren da ake kai wa a kasar ta nuna cewa hanyar da shugaba Muhammadu Buhari yake bi wajen kawo karshen ta’addanci a kasar ba mai bullewa ba ce.

KU KARANTA: Sarkin Tsafe ya bada umarnin cafko wadanda suka yi zanga-zanga a Zamfara

Kola Ologbondiyan, wanda shi ne Sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa, ya nemi Muhammadu Buhari ya tsige manyan hafsun sojin kasar.. Ologbondiyan ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da ‘yan jarida a jiya.

Babban Jami’in jam’iyyar yayi wa wadanda su ka rasa iyalan su a wannan hare-hare jaje inda yace dole hukuma ta dauki nauyin da ya dace wajen kare rayukan al’umma; tun daga jami’an tsaro na sojoji har zuwa mutanen gari.

Jam’iyyar ta PDP tace lokaci yayi da shugaban kasa zai sake duba lamarin gidan sojan kasar ya dauki matakin da ya dace, muddin dai babu wata makarkashiya a shirin da yake yi na yaki da ‘yan ta’adda da tsageru a Yankunan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel