Kyawawan tagwaye mata sun kafe a kan a kyalesu su auri miji guda, hoto

Kyawawan tagwaye mata sun kafe a kan a kyalesu su auri miji guda, hoto

Wasu kyawawan tagwaye mata 'yan asalin kasar Australia da aka yi ikirarin sun fi dukkan tagwaye na duniya kama da juna, sun bayyana yadda suke son auren saurayinsu amma doka tayi masu cikas.

Tagwayen, Anna da Lucy DeCinque, masu shekaru 33 a duniya, sun bayyana yadda suke burin auren saurayinsu, Ben Byrne, mai sana'ar gyaran motoci (bakanike), da suke soyayya tare tun shekarar 2012.

Sai dai dokar kasar Australia ta haramta wa 'yan kasar ta auren mace fiye da daya a karkashin dokokin aure da aka kirkira tun 1961, lamarin da ya zame wa tagwayen cikas.

'Yan matan sun bayyana a wani shirin gidan Talabijin na kasar Australia inda suka nemi a taimaka masu wajen warware wannan matsala dake damunsu.

Kyawawan tagwaye mata sun kafe a kan a kyalesu su auri miji guda, hoto
Kyawawan tagwaye mata sun kafe a kan a kyalesu su auri miji guda, hoto
Asali: Instagram

Da suke shaidawa dan jaridar dake hira da su matsalar su, Anna da Lucy sun ce, "akwai matsalar dake damun mu, muna son saurayinmu Ben kuma muna son aurensa amma dokar Australia bata amince namiji ya auri mace fiye da daya ba, yanzu ya zamu yi kenan?", suka tambaya.

A wani labarin na Legit.ng a nan gida Najeriya, kun ji cewar dalibai mata a jami'ar jihar Delta sun bayyana cewar sun hakura da saka karamin wando na mata (pant ko "dan kanfai" da Hausa) saboda yadda matsafa ke sace masu wannan sutura domin yin tsafin samun kudi.

DUBA WANNAN: Sanata Wamako ya yi yayyafin kudi ga magoya bayansa, hotuna

Matan dake karatu a jami'ar sun ce lamarin ya yi tsamarin da har ya kai ga matsafan da ake kira Yahooo Boys na tare mata su kuma tilasta su cire dab kanfansu ta hanyar nuna masu makami.

Lamarin satar dan kamfai na mata masu shekaru 14 zuwa 35 ya kai matakin da saida gwamnatin jihar ta tashi tsaye domin yaki da masu aikata wannan muguwar dabi'a.

Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewar farashin dan kamfai na budurwa kan kai kimanin Naira dubu dari uku da hamsin (N350,000), musamman idan akwai jinin al'ada a jikinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel