Jerin kyawawan ‘Yan matan da ake da su a gidan Kannywood

Jerin kyawawan ‘Yan matan da ake da su a gidan Kannywood

Legit Hausa ta leka zauren Kannywood inda ta kawo jerin tarin kyawawan matan da ke cikin harkar wasan kwaikwayon Hausa. Daga cikin wadannan ‘Yan mata da ake ji da su akwai Hadiza Gabon, Nafisa Abdullahi da sauran su.

Jerin kyawawan ‘Yan matan da ake da su a gidan Kannywood
Nafisat Abdullahi tana ‘Yan matan da ke tashe Kannywood
Asali: Facebook

Ga kadan daga jerin wadannan ‘Yan mata da Nairaland ta kawo:

1. Nafisat Abdullahi

Nafisat Abdullahi tana cikin ‘Yan matan da ake ji da su a Kannywood wanda ta rika tashe daga shigar ta harkar fim. Nafisat baka ce, kyakkyawa kuma siririya, son kowa kin wanda ya rasa. Nafisat shiru-shiru ce a fuska

2. Hadiza Gabon

Hadiza Aliyu (wanda aka fi sani da Gabon), kyakkyawa ce mai jiki da sura kuma fitatta a Kannywood. Budurwar tana cikin wadanda su ka shahara yanzu a Najeriya duk da cewa asalin ta mutumiyar kasar Gabon ce.

KU KARANTA: Musulma ta kawata gidan fasto don bikin Kirisimeti a Kaduna

3. Rahama Hassan

Rahama Hassan Rahama tana cikin wadanda ake ji da su a harkar fina-finan Hausa. ‘Yar wasar tayi karatu ne a Jami’ar Gwagwalada da ke Garin Abuja. Ilmin Rahama ya sa manyan masu shirya fim su ke rububin ta a Najeriya.

4. Jamila Nagudu

Fitacciyar Jaruma Jamila Nagudu tana cikin wadanda su ke tashe yanzu a Najeriya. ‘Yar wasar ta Kannywood ta na cikin kyawawan ‘Yan wasan kwaikwayo. Jamila ta fara kaurin suna ne a wani fim da tayi mai suna “Jamila da Jamilu”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng