2019: INEC ta sake bullo da dabarun magance magudin zabe

2019: INEC ta sake bullo da dabarun magance magudin zabe

A kokarinta na gudanar da sahihan zabuka da magance magudi da sayen kuri'u a shekarar 2019, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bullo da wasu dabaru na fasaha domin tattara sakamakon zabe da masu ruwa da tsaki zasu iya bibiya.

Kwamishinan INEC a jihar Benuwe, Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da jami'an 'yan sanda.

A cewar masu ruwa da tsaki, amfani da sabuwar fasahar tattara sakamakon zaben zata kara wa zaben 2019 kima da karbuwa.

Shugabannin jam'iyyun APC, PDP, LP, APGA da sauran su sun halarci taron bitar da aka yi a ofishin INEC na jihar Benuwe.

2019: INEC ta sake bullo da dabarun magance magudin zabe
Shugaban hukumar zabe; Farfesa Mahmood Yakubu
Asali: Depositphotos

INEC ta samar da sabbin dabarun ne domin magance irin matsalolin da hukumar ta fuskanta a zabukan da aka yi na baya-bayan nan a jihohin Ekiti da Osun.

DUBA WANNAN: Akwai mutanen da Allah ba zai bari su mulki Najeriya ba - Obasanjo

Da yake jawabi yayin taron, Okon Ene, kwamishinan 'yan sanda na jihar Benuwe, ya yi gargadi ga magoya bayan 'yan siyasa a kan lalata allunan talla da ba na jam'iyyar su ba.

Ya ce hukumar 'yan sanda zata dauki mataki a kan duk wanda ya samu da laifin tayar da fitina ko kokarin yin magudin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng