Hukumar 'yan sanda ta tura karin jami'ai Zamfara bayan harin Magami

Hukumar 'yan sanda ta tura karin jami'ai Zamfara bayan harin Magami

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta aike da karin sabbin jami'an 'yan sanda zuwa jihar Zamfara bayan harin da 'yan ta'adda suka kai a Magami

- Harin da 'yan ta'addan suka kai a ranar Asabar 22 ga watan Disambar 2018 aya yi sanadiyar rasuwar al'umma da dama

- Hukumar 'yan sandan ta ce sabbin jami'an 'yan sandan za suyi aiki tare da sauran hukumomin tsaro a jihar domin kawar da 'yan ta'addan

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce ta tura wasu karin jami'an ta zuwa kauyen Magami da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara bayan wasu 'yan ta'adda sun kashe mutane masu yawa a ranar Asabar.

Sabbin 'yan sandan da aka aike sun hada da jami'an sashin yaki da ta'addanci (CTU), jami'ai na musamman masu hana fashi da makami (FSARS) da kuma 'yan sandan sintiri wato Mobile Force.

'Yan sanda ta tura karin jami'ai Zamfara bayan harin Magami

'Yan sanda ta tura karin jami'ai Zamfara bayan harin Magami
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

Sanarwar da ta fito daga jami'in hulda da jama'a na hukumar, SP Mohammed Shehu a ranar Lahadi ta ce an karo sabbin 'yan sandan ne domin su taimakawa 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke jihar.

A yayin da ya ke mika sakon ta'aziyyarsa da iyalan wadanda suka rasu, Shehu tuni sabbin 'yan sandan sun iso kauyen kuma sun fara bin sahun 'yan ta'addan tare da sauran hukumomin tsaro.

Ya kara da cewa dukkan hukumomin tsaro da ke jihar za su cigaba da aiki tare har sai lokacin da aka samu zaman lafiya a kauyen.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta kuma ruwaito cewa mukadashin gwamnan jihar, Alhaji Sanusi Rikiji, shugabanin hukumomin tsaro na jihar, masu rike da sarautun gargajiya sauran al'umma ne suka hallarci jana'izar wadanda aka kashe a harin a ranar Lahadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel