Harkar tsaro: Shugaban 'Yan Sandan Najeriya ya amince a dauki mutane 10, 000 aiki

Harkar tsaro: Shugaban 'Yan Sandan Najeriya ya amince a dauki mutane 10, 000 aiki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris, ya tabbatar da zai dauki sababbin Jami’an ‘Yan Sanda 10, 000 aiki. IGP Idris ya tabbatar da wannan da kan sa.

Harkar tsaro: Shugaban 'Yan Sandan Najeriya ya amince a dauki mutane 10, 000 aiki
Za a kuma daukar 'Dan Sanda 10, 000 aiki bayan an yaye wasu
Asali: Depositphotos

A wajen wani taro da aka yi na yaye sababbin ‘Yan Sanda a Garin Kalaba a cikin Jihar Kuros-Riba, Ibrahim Idris, ya bayyana cewa sun fara shirin daukar wasu Ma’aikata. Wani babban Jami’in Hukumar ya wakilci IGP a wajen wannan taron.

Shugaban ‘Yan Sandan kasar, ta bakin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kuros-Riba, Mohammed Inuwa Hafiz, ya bayyana cewa Najeriya na kokarin daukar sababbin Jami’an tsaro ne domin cika sharudan da Hukumar UN ta kafa.

KU KARANTA: Ana kutun-kutun na kawo hatsaniya a zaben 2019 a Neja Delta

Majalisar dinkin duniya tace ya kamata ace akwai akalla ‘Dan Sanda guda 1, a cikin mutane 400, a kowace kasa domin a samu isasshen tsaro. Wannan ya sa Gwamnatin Buhari ta sake tashi tsaye domin ganin an wanzar da zaman lafiya a kasar.

Inuwa Hafiz ya kuma yi farin cikin ganin yadda aka yaye wasu kananan ‘Yan Sanda kwanan nan a Kalaba, a daidai lokacin da ake shiryawa zaben 2019. Kwanan nan ne dama Shugaban kasa ya ba IGP umarni ya samar da tsaro a zabe mai zuwa.

A baya kun ji cewa a fara rade-radin Shugaba Muhammadu Buhari zai karawa shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Kpotum Idris wa'adin mulki na kimanin watanni shidda domin ya shirya zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel