Ana kutun-kutun na kawo hatsaniya a zaben 2019 - Kungiyoyin Neja Delta

Ana kutun-kutun na kawo hatsaniya a zaben 2019 - Kungiyoyin Neja Delta

Wata kungiya ta masu fafatuka a Yankin Neja-Delta sun zargi wasu manyan ‘Yan siyasa a Najeriya su na yunkurin tara makamai a Kudancin Najeriya domin kokarin tada fitina a babban zabe mai zuwa na 2019.

Ana kutun-kutun na kawo hatsaniya a zaben 2019 - Kungiyoyin Neja Delta

‘Yan siyasa na yunkurin kawo rikici a zabe mai zuwa
Source: Depositphotos

Wasu tsagerun Neja-Delta sun fara nuna dar-dar game da zaben 2019 inda su kayi ikirarin cewa ‘Yan siyasa na boye manyan bindigogi a Garuruwan Ribas da Bayelsa da kuma Akwa-Ibom domin shirya jawo fitina a zaben shekara mai zuwa.

Kungiyoyin Neja-Delta sun fitar da wannan jawabi ne kwanaki inda su ka tabbatar da cewa yanzu haka an boye bingigogi sama da 48, 000 na AK 47 a wasu Yankunan Kudancin Najeriya. Za ayi amfani da wannan makamai ne wajen kashe-kashe.

Haka kuma Kungiyoyin sun zargi ‘Yan siyasa da yin hayar wasu ‘yan daba domin su murde zabe. Kungiyoyin su kace an shirya biyan wadannan ‘Yan iskan gari kudi N100, 000, yayin da za a biya manyan ‘Yan iskan Miliyan guda a duk ranar zabe.

KU KARANTA: Afenifere ta nuna akwai yiwuwar Yarbawa su bi Atiku a 2019

Wadanda su ka fitar da wannan jawabi sun hada da Kungiyoyi John Duku na Kungiyar Niger Delta Watchdogs and Convener of the Coalition of Niger Delta Agitators; da kuma Jomo Gbomo daga (Movement for the Emancipation of Niger Delta).

Sauran wadanda su kayi wannan ikirari sun hada da Kungiyoyin da su kayi fice a Neja-Delta irin su Niger Delta Avengers, Niger Delta Volunteers, da Bakassi Strike Force da kuma Kungiyar nan ta Niger Delta Warriors da wasu Kungiyoyi da-dama.

Kungiyoyin sun koka da cewa akwai yiwuwar rikici ya rincabe a Neja-Delta a zaben da za ayi a shekara mai zuwa saboda mugayen makaman da aka shigo da su Yankin kasar mai arzikin mai domin a rabawa Miyagu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel