FIFA Club World Cup: Madrid ta lallasa Al – Ain, ta sake daukar kofi

FIFA Club World Cup: Madrid ta lallasa Al – Ain, ta sake daukar kofi

A jiya ne mu ka samu labari cewa Kungiyar Real Madrid ta sake yin nasarar cin kofin Zakarun Turai na Duniya watau FIFA Club World Cup. Real Madrid ta doke Kungiyar Al – Ain ne a wasan karshe da ci 4-1.

FIFA Club World Cup: Madrid ta lallasa Al – Ain, ta sake daukar kofi
Kungiyar Real Madrid ta kafa tarihin da ba a taba gani ba
Asali: Twitter

Real Madrid ta lashe wannan kofi sau 3 kenan a jere, abin da ba a taba yi ba a tarihi. Haka kuma wannan ne karo na 4 da Kungiyar ta ci wannan kofi, hakan na nufin Real Madrid ta kerewa Abokan adawar ta na Kasar Sifen watau Barcelona.

Kungiyar Barcelona ta daga kofin sau 3 a tarihin ta, yanzu dai Real Madrid ta sha gaban Kulob din. Zakarun Turan na bana da bara da ma kuma bara wancan sun lallasa Kungiyar Al – Ain ne ta hannun Modric, Llorente da kuma Ramos.

KU KARANTA: Kungiyar Man Utd ta bayyana sabon Kocin ta na rikon-kwarya

Luka Modric ya fara barka ragar, kafin Marci Llorente ya ci wa Real Madrid kwallon sa ta farko. Haka kuma Sergio Ramos ya jefa ta 3. Tsukasa Shiotani ya ci wa Al – Ain kwallo guda, kafin wani ‘Dan wasan ta ya juya ya ci ragar sa da kan sa.

Real ta sake lashe Gasar na Intercontinental Cup a wannan shekara. Barcelona ce tayi nasara a Gasar a 2009, 2011 da kuma 2015. Daga 2014 kuwa kawo yanzu, Real Madrid ta ci kofin sau 4 kenan a 2014, 2016, 2017, da kuma shekarar 2018.

‘Yan wasan Real sun lashe kyaututtuka a Gasar. A Ingila kuma, kun ji cewa sabon kocin Kungiyar Manchester United, Ole Gunner Solskjaer ya dawo Manchester da kafar dama inda ya lallasa Kungiyar Cardiff a wasan sa na farko da ci 5-1.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel