‘Dan Majalisa, Abdulmumin Jibrin ya saye motoci domin yi wa Buhari kamfe a 2019

‘Dan Majalisa, Abdulmumin Jibrin ya saye motoci domin yi wa Buhari kamfe a 2019

Mun ji cewa Hon. Abdulmumin Jibrin wanda yake wakiltar Yankin Jihar Kano a majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ya bada gudumuwar motoci da-dama domin yakin neman zaben Buhari a 2019.

‘Dan Majalisa, Abdulmumin Jibrin ya saye motoci domin yi wa Buhari kamfe

Hon. Abdulmumin Jibrin ya ba APC gudumuwar motoci 150
Source: Depositphotos

Honarabul Abdulmumin Jibrin na mazabar Kiru da Bebeji ya raba motoci har 150 domin taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano yakin kamfe na tazarce a zabe mai zuwa.

‘Dan majalisar kasar wanda yayi fice wajen kokarin bankado badakalar da ake yi a majalisar tarayya ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita a karshen makon nan. Jibrin ya nuna cewa su na tare da Buhari da Ganduje a 2019.

KU KARANTA: Osinbajo ya fadawa Yarabawa ribar da za su samu idan su ka bi APC

Abdulmumin Jibrin ya tabbatar da cewa ya saye motoci kirar Volkwagen golf sababbi gal domin yakin neman zabe na APC watau Next Level. ‘Dan majalisar yace za su yi wa APC kamfe ne lungu-lungu a Jihar Kano a zaben badi.

Hon. Jibrin wanda aka dakatar daga majalisa shekarun baya saboda kokarin fallasa harkalar da ake yi a kan kasafin kudin kasar yace za su shiga sako-sako wajen ganin sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari kamfe a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel