'Yan Najeriya mazauna Indiya dake kurukuku a can na kira ga gwamnati da ta jiyo kukansu

'Yan Najeriya mazauna Indiya dake kurukuku a can na kira ga gwamnati da ta jiyo kukansu

- 'Yan Najeriya mazauna Indiya masu neman karatu ne da masu neman kudi

- An san Indiyawa dai da mugun kabilanci kan bakake

- Suna kulle yaran Najeriya kan kananan laifuka

'Yan Najeriya mazauna Indiya dake kurukuku a can na kira ga gwamnati da ta jiyo kukansu

'Yan Najeriya mazauna Indiya dake kurukuku a can na kira ga gwamnati da ta jiyo kukansu
Source: UGC

Wadansu 'yan Najeriya mazauna Indiya sun koka kan yadda aka kulle 'yan-uwansu shekaru biyu babu wani jami'in Najeriya da ya kula ya sanya baki aji makomarsu a ofishinn jakadancin kasar, duk kuwa da laifukansu basu taka kara sun karya ba.

A cewarsa dai, matasan da kasar ta Indiya ke kamawa, tana ware bakake ne 'yan kasashen Afirka, musamman na Najeriya, kan kananan laifuka da suke addabar yankunan biranen kasar.

Dama dai an san 'yan NAjeriya da irin wannan laifuka a sassan duniya, inda muka yi kaurin suna wajen karya doka, wanda gwamnati ke kokarin wayar da kan 'yan kasa da su daina.

DUBA WANNAN: Aghanistan zata koma hannun Taliban bayan janyewar Amurka

Laifin dai da Indiya take kama 'yan Najeriya dashi, banda na 'yann sace-sace, akwai na sane, da fitsara da ma cuwa-cuwa, a wasu lokutan kuma, har in biza ma tayi espaya ana iya kama mutum.

Da labari ya kai ofishin jakadancin Najeriya a Birnin Delhi kan batun, bayan da matasan da suka shekara biyu a kulle, kudaden da suka bari ya kare kan lauyoyin da aka dauko musu na kasar ta Indiya, sai wai ma'aikatan jakadancin suma suka ce a hada musu kudi kafin su kai ziyara jihohin da aka kulle 'yan Najeriyar, inji mai kwarmaton.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel