Yadda Adams Oshiomhole ke hada shugaba Buhari fada da gwamnoni, ana tsaka da neman tazarce

Yadda Adams Oshiomhole ke hada shugaba Buhari fada da gwamnoni, ana tsaka da neman tazarce

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayan shi ga Uzodinma

- Ku guji masu hada hotunan su da na Buhari, akwai na gaibu

- Buhari jam'iyyar APC yake, bashi da wata jam'iyyar daban

Yadda Adams Oshiomhole ke hada shugaba Buhari fada da gwamnoni, ana tsaka da neman tazarce
Yadda Adams Oshiomhole ke hada shugaba Buhari fada da gwamnoni, ana tsaka da neman tazarce
Asali: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayan shi ga Dan takarar gwamnan jihar Imo karkashin jam'iyyar APC, Sen. Hope Uzodinma.

Majiyar mu ta gano cewa shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya sanar da hakan a bude yakin neman zaben Uzodinma a Owerri ranar juma'a.

Ya hori mutanen jihar Imo dasu nisanta kansu daga jam'iyyun da basu sani ba, wadanda ke hada hotunan su da na shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa Uzodinma ne kadai Dan takarar da Buhari ke goyon baya a takarar gwamna.

DUBA WANNAN: Amurka zata janye daga Afghanistan, bayan sulhu da Taliban da ta yaka tun 2001

"Wadanda ke hada hotunan su da na Buhari saboda su samu jama'a, jabu ne. Jam'iyyar Buhari APC ce. Buhari na goyon bayan Uzodinma a matsayin Dan takarar gwamnan jihar Imo. Mun kawo muku sakon buri ne ba na jaje ba. Duk da abubuwa sun tafi ba daidai ba a kwanakin nan, mun zo ne mu tabbatar muku da cewa zamu dawo ma da mutanen jihar nan mulkin su."

Ana dai ganin cewa da yawan gwamnonin da uwar jam'iyya a APC ta hana takara, ko ta hana yaransu tikiti da tuta, zasu tadiye kafar jam'iyyar a jiharsu, ya zuwa yanzu dai gwamnoni da suka shaqa sun hada da na Legas, na Zamfara, na Imo da na Ogun, da kuma wasu jiga-jagan a Kano.

"Gwamnatin mai zuwa zata kawo cigaba ga yan jihar Imo. Yau ba ranar gama bace, ranar dawo da burirrika ne. Kuna da dalilan neman canji," inji shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel