Sojoji sun dakile wata sabuwar harin da 'yan bindiga suka kai a Benue

Sojoji sun dakile wata sabuwar harin da 'yan bindiga suka kai a Benue

Kwamandan sojojin Najeriya na atisayen Operation Whirl Stroke (OPWS), Manjo Janar Adeyemi Yekini ya ce dakarunsa sunyi nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a wasu sassan karamar hukumar Logo da ke jihar Benue.

A sanarwar ta da bayar a ranar Juma'a yayin hirar da manema labarai a Makurdi, Janar Yekini ya ce dakarun na OPWUS sunyi arangama da maharan ne wani sumame da suka kai tun daren Alhamis har zuwa safiyar Juma'a.

Sojoji sun dakile wata sabuwar harin da aka kai a Benue

Sojoji sun dakile wata sabuwar harin da aka kai a Benue
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An gurfanar da wani matashi a kotu saboda saduwa da akuya

Ya yi bayanin cewa a yayin samamen, dakarun sojin sun gano wani sansanin 'yan bindiga a kusa da gabar River Benue da ke karamar hukumar Logo inda ya ce wasu daga cikin 'yan bindigan sunyi kokarin tsallakawa Jihar Nasarawa ta cikin ruwa amma kwalekwalensu ya kife yayin musayar wuta.

"Akwai yiwuwar wasu daga cikin 'yan bindigan sun mutu a yayin arangamar amma babu wani daga cikin sojojin mu da ya samy rauni kuma babu farin hula da aka kashe sakamakon atisayen," inji shi.

Kwamandan sojojin ya yi kira da al'umma suyi watsi da wasu labarun karerayi da ake yadawa wai an kashe wasu fararen hula sakamakon arangaramar da sojin su kayi da dakarun sojin.

Ya kara da cewa, "Jita-jitar da wasu ke yadawa wai makiyaya 'yan bindiga sun kashe mutane hudu ko fiye da haka a karamar hukumar Logo na jihar Benue ba gaskiya bane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel