A Siyasa babu dan gida, sai wanda ra'ayinku yazo daya, siyasar Kano a yau

A Siyasa babu dan gida, sai wanda ra'ayinku yazo daya, siyasar Kano a yau

- Kano dai tafi kowacce jiha a Najeriya iya juya siyasa mai bangarori

- Kowanne gida a Kano yana da yaransa da jigo

- Wasu sunyi batan-bakatan-tan kamar jemagu

A Siyasa babu dan gida, sai wanda ra'ayinku yazo daya, siyasar Kano a yau

A Siyasa babu dan gida, sai wanda ra'ayinku yazo daya, siyasar Kano a yau
Source: Facebook

A makon nan dai, siyasar Kano, ta sake sauya salo, tun bayan da tsohon mataimakin gwamnan Kano ya bar jam'iyyarsa da kujerarsa ya koma gidan Kwankwasiyya a PDP, domin a bashi takarar kujerar da gwamnan yake kai, watau Ganduje.

Sai dai, Farfesa Hafiz, bai sami wannan ba a wajen abokinsa shaqiqi, Sanata Rabiu Kwankwaso, wadda hakan tasa yayi batan bakatan-tan.

Ana tsaka da haka kuma, sai bidiyo ya fito, na gwamnan yana amsar daloli a hannun wasu da ba'a nuna fuskarsu ba, wadanda masu sharhi suka ce 'yan Kwangila ne masu neman fada, lamari da ya dagula wa Ganduje lissafi, ta kai su har gaban kotu.

Sai kuma kwatsam, majalisa ta bude bincike, lamari da ke nuni da watakil gwamnan ya rasa kujerarsa in aka tabbatar kudin da yake karba cin hanci ne. Koma dai menene an karya doka, domin kuwa, a dokar Najeriya ba'a yarda mutum ya rike kudi tsababa a hannu ba, sai dai ya aika su banki, don haka akwai karya dokar 'Money Laudering'.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

Wannan kuwa zai bada dama sabon mataimakin gwamna Dr. Gawuna, ya amshe kujerar gwamna, cikin sauki, wadda hakan ke nuna lallai Farfesa Hafiz, yayi azarbabi na barin gwamnati, kuma gashi bashi nan bashi can.

Yanzu dai, ana tsaka da wannan, sai kuma ga tsohon na biyun ya dawo cikin jam'iyya, ya tuba ya baro maigidansa Kwankwaso. Wasu na gani kujerar Sanata wadda Mal. Ibrahim Shekarau ke nema ya dawo nema, wadda a yanzu Sanata Kwankwaso ne ke kai.

A gefe daya kuma, wasu 'yan Kwankwasiyya na ta sauyin sheqa, suna komawa bangaren gwamnati, wasu kuma, suna zuwa kamun kafa Abuja.

Gidajen dai na siyasar, biyu ne, Na Malam Ibrahim Shekarau, sai na Rabiu Musa Kwankwaso, kujerar gwamna dake gidan Kwankwaso sai ta subuce, ta dawo bangaren Malam Shekarau, ana kuwa sa rai, duk inda kujerar gwamna take, nan ke jagora a jihar.

Hasali ma, wasu na ganin kamar shima tsohn Gwamna Kwankwason ya fara shinshinar komawa gida bangaren Buhari, bayan da bidiyon gwamnan ya fita, bidiyo wanda aka ce ya bakantawa iyayen tafiya a APC Abuja rai, suna kuwa jira a gama zabe su ajje gwamna a tasha ta hannun majalisa, su nemo sabo mai tsarkin hannu, a raka dashi haka nan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel