Atiku zai raba kan 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa - Miyetti Allah

Atiku zai raba kan 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa - Miyetti Allah

- Shugaban Miyetti Allah, na jihar Benue Garu Gololo ya soki dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar bisa jingina kashe-kashe da akeyi ga shugaba Buhari

- Gololo ya ce Atiku Abubakar ya fara raba kawunnan 'yan Najeriya tun kafin ya zama shugaban kasar Najeriya

- Gololo ya ce tun kafin shugaba Muhammadu Buhari ya hau mullki ana samun rikici tsakanin makiyaya da monoma a wasu sassan kasar

Jagoran kungiyar makiyaya na Miyetti Allah Cattle Breeders Association reshen jihar Benue, Garu Gololo ya soki dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP inda ya ce Atiku Abubakar zai raba kan 'yan kasa muddin aka zabi shi shugaban kasa.

Gololo ya yi wannan maganar ne a ranar Alhamis yayin da ya ke mayar da martani kan kalaman da mai magana da yawun kungiyar kamfen din Atiku, Phrank Shaibu ya yi a farkon wannan makon inda ya ce za a samu karin kashe-kashen mikiyaya idan aka zabi shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Atiku zai raba kan 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa - Miyetti Allah
Atiku zai raba kan 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa - Miyetti Allah
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa

Shugaban na Miyetti Allah ya ce babban kuskure ne Atiku ya fadi wannan kalmar saboda ba fulani makiyaya ne kadai suke samun rashin jituwa da manoma ba.

Ya ce, "Ya ce mu makiyaya fulani ba mu kashe mutane kuma tun kafin Buhari ya hau kan mulki ana samun rikici tsakanin makiyaya da manoma a Benue, Taraba, Nasarawa, Adamawa da wasu jihohin Najeriya.

"Na ji takaicin abinda Atiku ya fada domin ya riga ya raba kan al'umma tun kafin ya samu mulki. Buhari ba shine ya janyo rikicin makiyaya ba, shima dan Najeriya ne kuma 'yan Najeriya ne suka zabe shi kuma nayi imanin za su sake zabensa a shekarar 2019."

Gololo ya tambayi tsohon mataimakin shugaban kasar ko makiyaya ne ke kashe-kashe a lokacin da ya ke mataimakin shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel