Hukumar NCC zata dawowa da kowa duk kudinsu da kamfanin waya suke sacewa

Hukumar NCC zata dawowa da kowa duk kudinsu da kamfanin waya suke sacewa

- Kamfunnan wayar salula sun dade suna sace kudin kwastoma

- Layukan wayar suna hadiyar kudi ba kakkautawa

- NCC ta gano hanyoyin da suke bi

Hukumar NCC zata dawowa da kowa duk kudinsu da kamfanin waya suke sacewa
Hukumar NCC zata dawowa da kowa duk kudinsu da kamfanin waya suke sacewa
Asali: Twitter

Hukumar da doka ta kafa, wadda zata bi dukkan koke da hakkokin masu amfani da layukan salula, irinsu MTN, Airtel, 9-Mobile da Glo, wadanda a lokuta da dama ke sace wa mutane kudinsu a waya, ta gano sabuwar hanyar da suke sace kudaden mutane daga kudin katinsu.

Hukumar, ta sha alwashin dawowa da duk wanda aka sacewa kudi, ko ya sani, ko bai sani ba. Hanyoyin da ake bi a sace kudin kuwa, sun hada da; kwashe kudin kati, dauke kudin VAS, da ma cire kudi kan abun da kwastoma bai saya ba.

DUBA WANNAN: Amurka ta sake aiko kudin gudummawa ta daloli ga jami'an tsaro don zaben 2019

Nnamdi Nwokike ne kakakin hukumar, wanda ya tabbatar wa da manema labarai lamarin, wanda yace sun bincika tsawon shekaru biyu kenan.

Cikin wayau dai, misali MTN, na sake kwashe maka kudi ta saya maka wani tsari, ko ta sai maka waqa, ko data wanda ka taba saya, wai da sunan kwamfiyuta ce tayi maka. In dai ka taba saya koda sau daya sai su kwashe watanni suna saya maka, kuma qememe in ka rubuta STOP zuwa 131 sai text din yaki shiga.

Hukumar ta sanya dokar yanzu sai an tambaye ka ko kana son ka sake sayen wannan tsari, sannan kuma duk wanda aka sacewa kudi da amara irin wannan sai an dawo musu dashi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel