An zagaye APC a jihar Obasanjo: Dan takarar da gwamnan APC ya tsayar a wata jam'iyyar ya tasamma lashe zabe

An zagaye APC a jihar Obasanjo: Dan takarar da gwamnan APC ya tsayar a wata jam'iyyar ya tasamma lashe zabe

- Dan takarar gwamnan jihar Ogun a karkashin jam'iyyar APM ya kaddamar da yakin neman zaben shi

- Yace yana goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Ya Kwatanta Amosun da madubin dubawa kuma shugaba nagari

An zagaye APC a jihar Obasanjo: Dan takarar da gwamnan APC ya tsayar a wata jam'iyyar ya tasamma lashe zabe

An zagaye APC a jihar Obasanjo: Dan takarar da gwamnan APC ya tsayar a wata jam'iyyar ya tasamma lashe zabe
Source: Depositphotos

Dan takarar gwamnan jiha karkashin APM, Adekunle Akinlade, ya kaddamar da yakin neman zaben shi a ranar Alhamis.

Bikin wanda akayi a stadium din Moshood Abiola a Abeokuta, ya samu halartar magoya bayan shi daga kananan hukumomi 20 na jihar da kuma shuwagabannin jam'iyyar.

Mista Akinlade ya bar jam'iyyar APC mai mulki bayan da Gwamnan jihar, Ibikunle Amosun, ya kasa tsayar dashi a matsayin Dan takarar jam'iyyar a jihar. Hakan ya jawo manyan yan jam'iyyar sun bar ta a jihar da kuma dakatar da zababbun jam'iyyar APC na jihar daga shugaban jam'iyyar na kasa Adams Oshiomhole.

Mista Amosun, wanda ke neman kujerar majalisar dattawa, yace duk da komawar mataimakan shi zuwa sabuwar APM, zai cigaba da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari don ganin komawar shi kujerar shi a 2019 amma yana adawa da Dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC.

Shugaban jam'iyyar ta kasa, Yusuf Mamman, yayin mika tutor jam'iyyar ga Mista Akinlade, yace jam'iyyar na yin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019. Ya taya yan jam'iyyar murna, da yawan su daga APC, kare da cewa sunyi zurfin tunani na komawa APM.

DUBA WANNAN: Yarinyar nan da ta tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook

Jami'in yayi kira ga sababbin yan jam'iyyar dasu hada kansu don ganin sunyi nasara a zabe mai gabatowa.

Babban daraktan yakin neman zaben, Sarafa Ishola yace jam'iyyar ta fara ne don ta dore.

Tsohon ministan ya hori yan jam'iyyar dasu shirya don samun nasara nan gaba. Yayi kira ga yan jam'iyyar dasu yi kokari gurin nasarar jam'iyyar a kujerun da suke nema.

Mista Akinlade yace tutar jam'iyyar da aka mika mishi zata kai ga gwamna Ibikunle Amosun na jam'iyyar APC don mika ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin alamar goyon bayan jam'iyyar gareshi.

Ya jinjiinawa Mista Amosun, wanda ya kwatanta a matsayin madubin dubawa kuma shugaba nagari.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel