Wani Ma’aikacin banki ya saci N500, 000 daga asusun Jama’a a Legas

Wani Ma’aikacin banki ya saci N500, 000 daga asusun Jama’a a Legas

Mun ji labari cewa wani Matashi mai shekara 35 da yake aiki a wani karamin banki mai suna ACCION Microfinance Bank a Legas, yana hannun hukuma bisa zargin cewa ya sace kudin Jama’a daga bankin.

Wani Ma’aikacin banki ya saci N500, 000 daga asusun Jama’a a Legas
Ana zargin wani Ma’aikacin banki da satar kudi daga asusun mutane
Source: Depositphotos

Daily Nigerian ta rahoto cewa wani Ma’aikacin banki mai suna Bashiru Odunukan yana fuskantar shari’a a gaban Alkali bayan da ake zarge shi da laifin satar kudi har N553, 500 daga hannun wasu da su ka nemi bashin banki.

Bashiru Odunukan yana aiki ne da bankin ACCION Microfinance da ke wani kauye a cikin Garin Legas. Ana tuhumar Odunukan da yin gaba da kudin da wasu Mutane su ka karbi bashi ne a cikin Watan Nuwamban da ya wuce.

Thomas Nuruddeen, wanda shi ne Lauyan da ke karar Odunukan, ya fadaawa kotu cewa, wannan Ma’aikacin banki yayi awon gaba da kudin wasu Bayin Allah zuwa cikin aljihun sa a lokacin da su ka zo neman aro a hannun bankin.

KU KARANTA: Access Bank ta karbe Diamond Bank saboda karancin jari

Ba a gano wannan danyen aiki da Jami’in bankin ya tafka ba, sai bayan da aka zo ana bincike kwanaki. Wani mai bin diddiki mai suna Ayodeji Olulode da aka turo zuwa bankin da ke Yankin Sango-Ota ne ya bankado barnar da aka yi.

Yanzu dai an maka wannan Ma’aikacin banki a gaban wani kotun majistare da ke cikin Legas. Alkali mai shari’a K. B Ayeye ya bada belin wanda aka kara a kan kudi N200, 000 kafin a cigaba da shari’a Watan Maris din shekarar badi.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta bayyana cewa satar kudin jama’a daga asusun su a banki, ya sabawa sashe na 257 na dokar Jihar Legas. Ana iya daure wanda aka kama da wannan mugun laifi a gidan yari na tsawon shekaru 7.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Online view pixel