Malamin Ingilishi a Kasar Amurka yace akwai rauni a Turancin Farfesa Osinbajo

Malamin Ingilishi a Kasar Amurka yace akwai rauni a Turancin Farfesa Osinbajo

Mun samu labari cewa wani kwararren Malamain Ingilishi a wata Jami’a a Kasar Amurka yace akwai raunin harshe a cikin wani jawabi da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi kwanaki.

Malamin Ingilishi a Kasar Amurka yace akwai rauni a Turancin Farfesa Osinbajo

Kperogi ya ci gyaran Turancin Mataimakin Shugaban kasa
Source: UGC

Kwankin baya ne Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gana da wasu ‘Yan Najeriya inda ya sha alwashi cewa Gwamnatin su ta Shugaba Buhari za tayi bakin kokarin ta wajen ganin ta kai Najeriya ga ci, kafin cikar wa’adin ta.

Farouk Kperogi wanda babban Malami ne a Jami’ar Kensas ta Amurka wanda ya kware a harkar harshen Ingilishi ya bayyana cewa akwai gyare-gyare a jawabin da Yemi Osinbajo yayi a lokacin da yake jawabi game da shirin #NextLevel.

Dr. Kperogi wanda ya saba yin rubutu a bangaren Nahawu da ma sha’anin siyasa yace nahawun Mataimakin Shugaban kasar cike yake da bankaura. Babban Malamin na Ingilishi yayi wa Yemi Osinbajo wannan gyara ne a shafin Tuwita.

KU KARANTA: Farfesa Osinbajo bai da ilmin tattalin arziki inji Atiku

Malamin da ya dade yana koyar da Nahawun Ingilishi a Jami'ar Jihar Kensas ta Kasar Amurka yake cewa bai kamata Yemi Osinbajo ya rika yin irin kure-kuren da yayi a matsayin sa na babban Farfesa kuma wanda ya karanta harkar shari’a ba.

Ga dai abin da Kperogi ya fada da harshen Ingilishi a shafin na sa inda ya ci gyaran Mataimakin Shugaban kasar:

“First get your basic grammar right. You're a lawyer, after all. It should be, "For President Muhammadu Buhari and ME," NOT "For President Muhammadu Buhari and I." You focus "ON," not "about" people. Finally, it's "THE/A majority of our people," not "majority of..."

Bayan nan kuma dai Masanin harkar luggan ya koka da cewa abin da Mataimakin Shugaban kasar yake fada sam ba gaskiya bane inda ya nuna cewa yaudarar al’umma kurum Gwamnatin Shugaba ta ke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel