Watakila tsohon ‘Dan wasa Gunnar Solskjaer ya zama sabon Kocin Manchster United

Watakila tsohon ‘Dan wasa Gunnar Solskjaer ya zama sabon Kocin Manchster United

Labari ya zo mana daga Jaridun Kasar waje cewa Kungiyar Manchester United tayi kuskuren bayyana wanda zai maye gurbin Kocin da ta sallama daga aiki jiya da safe watau Jose Mourinho a shafin ta.

Watakila tsohon ‘Dan wasa Gunnar Solskjaer ya zama sabon Kocin Manchster United

Da alama Gunnar Solskjaer zai rike Man Utd na wani ‘dan lokaci
Source: Facebook

Kungiyar ta Manchester United tayi kuskuren fadin sunan Ole Gunnar Solskjaer a matsayin sabon Kocin ta rikon kwarya kafin karshen kakar bana. Kungiyar ta bayyana wannan ne a shafin ta na yanar gizo a Ranar Talatan nan daddare.

Sai dai jim kadan bayan Kulob din ta bayyana wannan, tayi wuf ta goge sakon. Kafin nan dai dubban Jama’a sun samu wannan labari. Kulob din ta saki wani bidiyo ne na tsohon ‘Dan wasan ta Solskjaer wanda tace zai gaji Mourinho.

KU KARANTA: Zidane zai nemi ya maye gurbin Jose Mourinho a Manchester

Kulob din ta saki wani bidiyo ne da tsohon ‘Dan wasan gaban na ta ya ci mata wani wasa a filin Camp Nou, shekaru 20 da su ka wuce. A wancan lokaci, Manchester ta lashe Gasar Zakarun Nahiyar Turai da kuma Gasan gida na Firimiya.

Manchester tayi maza ta goge wannan bidiyo daga shafin ta, amma har Firayim Ministar kasar Norwegia watau Kasar da Kocin na yanzu ya fito, ta fara aika masa sakon taya sa murnar samun wannan babban aiki da yayi.

Erna Solberg ta aikawa Ole Gunnar Solskjaer sakon ne ta shafin ta na Tuwita kafin Kulob din ta goge wannan sanarwa. Solskjaer ya ci wa United kwallo 91 cikin wasanni 235 sannan kuma ya horas da Yarn Kungiyar da wasu kananan Kulob.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel