Bayan da Access bank ya hadiye bankin Diamond, kasuwar hada-hadar hannayen jari ta daga

Bayan da Access bank ya hadiye bankin Diamond, kasuwar hada-hadar hannayen jari ta daga

- A tsari, sai banki ya kai wasu biliyoyi CBN za'a bashi lasisi

- Muddin ya kasa, akan kwace bankin daga masu shi a baiwa wadanda zasu iya farfado dashi

- Bankunan Najeriya sun dade suna adi tashi tun bayan hana su kudin gwamnati

Bayan da Access bank ya hadiye bankin Diamond, kasuwar hada-hadar hannayen jari ta daga

Bayan da Access bank ya hadiye bankin Diamond, kasuwar hada-hadar hannayen jari ta daga
Source: UGC

A baya, manya a gwamnati kan ajje kudin ma'aikatun su a bankunan 'yan kasuwa, domin a juya a basu wanii kaso, kamar dai 10% na kudin, a matsayin la'ada, bayan kudaden sun shekara, wanda hakan ke sanya a sami tsaiko a kashe kudin gwamnati.

Sai bayan da shugaba Buhari ya hau, sai ya kwace dukkan kudaden na ma'aikatu, ya mayar lalita ta bai daya ta gamnati, wanda hakan ya bar bankunan fanko babu jari babu kudin harka.

Sai dai bayan wasu bankunan sun farfado, wasu sun kasa, inda suka fara neman agaji, misali shine yadda AMCON ta kwace SKYE bank ya mai da shi Polaris.

DUBA WANNAN: Bayan yankunan Kano da Kaduna, na Maiduguri ma sun koka da tsadar wutar lantarki

Shi kuma Diamond bank, tun kafin a kai ga haka, sai ya nemi hadewa da Access bank, wanda yake da kwari a tsakanin tsarorinsa.

Sayar da wannan banki ke da wuya, sai kasuwannin hannayen jari na Najeriya suka daga, wanda ke nufi da lamarin ya kwantar wa da masu kadarori a bankunan da ma masu ajiya hankali.

A jiya kadai, a NSE, watau Nigerian Stock Exchange, an sayar da share 70.98m ta bankin. wadda ta kama kusan N72.64m a hada-hada 129. An kuma baiwa duk mai hannnun jari a Diamond bank din, hannayen jari a Acess bank, koda yake an zaftare fin rabi, saboda darajar bankunan ta banbanta.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel