Saudia tayi Allah-wadai da Tir din da majalisar dattijan kasar Amurka tayi mata kan kisan Khashoggi

Saudia tayi Allah-wadai da Tir din da majalisar dattijan kasar Amurka tayi mata kan kisan Khashoggi

- Majalisar Dattawan Amurka tayi tir da Mamlakar Saudiyya

- Masarautar Saudiyya tayi Tir da Tir din da Turawa ke jeho mata

- Har yanzu babu gawar dan jaridar

Saudia tayi Allah-wadai da Allah-wadai na majalisar kasar Amurka

Saudia tayi Allah-wadai da Allah-wadai na majalisar kasar Amurka
Source: Depositphotos

Bayan da ta tabbata, cewa kashe Khashoggi aka yi a Turkiyya, bayan da aka yi masa-shigo-shigo ba zurfi, aka tsira masa allurar mutuwa, aka kuma yi gunduwa-gunduwa dashi, inda daga bisani aka narka gabobinsa a acid, Amurka tace ta gano wanda yayi kisan.

Majalisun, da hukumar leken asirin Amurka, da ma na Turkiyya, sunce Yarima bin Salman ne yayi kisan, kuma sunyi tir dashi, da ma kuma barazanar bazasu bari a ci gaba da sayar masa makamai don yakar Yemen ba.

A taron G20 dai da aka yi a kwanan nan, MBS ya sha kunya, bayan da dukkan shuwagabanni da 'yan jarida, wadanda a baya ke haba-haba dashi, suka dauke kansu suka ki kula shi. Bidiyo ya nuna yadda ya shaqa, daga gwalewar da ake ta masa a fili.

DUBA WANNAN: Masu gudun hijira 250,000 ne suka koma gidajensu a jihohin tsakiyar Najeriya a bana

Sai dai masarautar ta Saudiyya a gwamnatance, tace wannan cece-kuce, da ma barazana kan kisan ba bisa qa'ida ba, da cewa katsalandan ne duniya ke musu da shisshigi.

Shugaban Amurka dai yaqi ya sahalewa majalisun da ma hukumomin leken asirinsa kan daukar gwaggwafan mataki a lamarin.

Amurka na jin dadin mai me araha da Saudiyya ke basu, da kuma cinikin sayen makamai da jiragen yaqi.

A karshe dai, Khashoggi ya mutu, kuma an narkar da komai nasa babu ko hakori, an kuma yi fuloshin ruwan a masai.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel