Bayan yankunan Kano da Kaduna, na Maiduguri ma sun koka da tsadar wutar lantarki

Bayan yankunan Kano da Kaduna, na Maiduguri ma sun koka da tsadar wutar lantarki

- Wasu masu amfani da wutar lantarki a jihar Maiduguri sun koka da yawan kudin da kamfanin rarraba wutar lantarki na Yola ke cajin su

- Masu amfani da wutar lantarkin sunce cigaban abun fargaba ne

- Hakan zai iya wahalar da talaka

Bayan yankunan Kano da Kaduna, na Maiduguri ma sun koka da tsadar wutar lantarki
Bayan yankunan Kano da Kaduna, na Maiduguri ma sun koka da tsadar wutar lantarki
Asali: UGC

Wasu masu amfani da wutar lantarki a jihar Maiduguri sun koka da yanda kamfanin rarraba wutar lantarki na Yola ke tsawwala musu.

Wasu daga cikin mazauna garin da suka zanta da ofishin dillancin labarai a ranar talata sun Kwatanta cigaban da abin damuwa, kare da cewa hakan zai takurawa talaka saboda hakan na datse aiyukan cigaba na mutane.

Esther Chukwuma, daya daga cikin masu amfani da wutar ta Kwatanta sabon salon na tsawwala music kudi da kamfanin rarraba wutar lantarki ta fito dashi a matsayin abin jaje.

DUBA WANNAN: Tsage gaskiya: Aikin waye kawo jirgin kasa daga Abuja zuwa jihohi?

"Bill dina na nuna nayi amfani da unit 605 a watan Nuwamba kuma suka case ni akan Naira 14,000 a maimakon Naira 6,500.

Suna karbar kudina akan wutar da ba sha ba. Da rana ina shagona, da dare ne kadai nake amfani da wutar. Ina da metre mai kati a shagona, a wata Naira dubu biyu nake kashe mata.

Toh ta yaya gidan da bana amfani da wuta sai da dare za'ace na sha 14,000. Ganin nan a ofishin su ina bukatar bayani, " inji ta.

Fatima Musa, tayi kake akan an bata bill din 15,000 a maimakon 5,000 da ake bata a wata sannan babu wani bayani a kai. Tace rashin meter mai kati ne ke jawo hakan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel